Kano: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari, an Yi Garkuwa da Mutane

Kano: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari, an Yi Garkuwa da Mutane

  • Wasu 'yan bindiga sun yi ta'asa a wani hari da suka kai a jihar Kano da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
  • Miyagun 'yan bindigan sun yi awon gaba da wani mutum daya bayan sun kai hari a karamar hukumar Kumbotso
  • Jami'an tsaro na 'yan sanda sun bazama wajen ganin sun kubutar da mutumin bayan samun rahoton harin na 'yan bindiga

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun sace wani mazaunin unguwar Zawachiki da ke cikin karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa wanda aka sace ɗin mai suna Aminu Abdullahi, an yi awon gaba shi ne da safiyar Asabar da misalin karfe 11:30 na safe.

'Yan bindiga sun sace mutum 1 a Kano
Hoton jami'an 'yan sanda a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Mazauna Katsina sun karyata ikirarin gwamnati na kubutar da su daga hannun 'yan ta'adda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun kai hari a jihar Kano

Maharan dai sun sace mutumin ne bayan sun dira cikin unguwar ba zato ba tsammani.

Wata majiya da ke kusa da lamarin ta bayyana cewa an kai rahoton satar ne ga jami’an ‘yan sanda da misalin karfe 7:45 na safiyar Lahadi.

Bayan samun rahoton, sai DPO na Kumbotso ya jagoranci wata tawagar sintiri zuwa wurin domin bincike da kuma kokarin ceto wanda aka sace.

Majiyoyi sun kara da cewa ɗan wanda aka sace, wanda ya kasance a wurin lokacin da lamarin ya faru, ya bayar da bayanai masu mahimmanci ga jami’an tsaro domin taimaka musu wajen gudanar da bincike.

Lamarin satar mutane na ci gaba da zama babban ƙalubale a wasu sassan kasa nan, ciki har da Kano, inda ake ganin irin wannan ayyukan ba kasafai suke faruwa ba idan aka kwatanta da jihohin da ke Arewa maso Yamma kamar Zamfara, Katsina da Kebbi.

Kara karanta wannan

Kwale kwale ya kife da mutanen da ke tserewa harin 'yan bindiga a Sokoto

Duk da haka, wannan hari ya haifar da tsoro da damuwa a zukatan mazauna unguwar Zawachiki, inda suka fara nuna fargaba kan tsaron rayuwarsu da dukiyoyinsu.

'Yan bindiga sun kai hari a Kano
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta karin wasu labaran kan 'yan bindiga

'Yan bindiga sun kashe mutane a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin ta'addanci a jihar Plateau.

Miyagun 'yan bindigan sun kashe mutane biyar tare da cinnawa gidaje da dama wuta a harin da suka kai a wani kauye na karamar hukumar Mangu.

Dakarun sojoji sun kai daukin gaggawa bayan samun rahoton lamarin, wamda hakan ya sanya suka yi artabu mai tsanani, inda daga karshe suka samu nasarar fatattakarsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng