Kano: Jami'an NDLEA Sun Cafke Matashi da Tramadol 7,000 daga Legas
- Hukumar da ke yaki da ta'ammali da miyagu kwayoyi NDLEA, reshen jihar Kano ta cafke wani matashi da kwayoyin Tramadol
- Mai magana da yawun hukumar, Sadiq Muhammad Maigatari ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da ya raba ga manema labarai
- Ya bayyana cewa jami'an hukumar sun gani kwayoyin duk da dabarar da matashin ya yi amfani da ita na kauce wa dakarunsu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA, ta samu nasara a fafutikar ta da safarar miyagun kwayoyi a jihar Kano.
Mai magana da yawun hukumar, Sadiq Muhammad Maigatari ya shaida wa manema labarai cewa sun samu nasarar damke wani matashi mai shekaru 29 mai suna Adamu Yusuf.

Kara karanta wannan
'Lokaci ya yi da za a dauki mataki,' ACF ta shiga takaicin yadda ake zubar da jinin 'yan Arewa

Source: Facebook
A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin 25 ga watan Agusta, 2025, ana iya ganin tarin kwayoyin masu launi daban daban da aka kunshe a leda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NDLEA ta yi babban kamu a jihar Kano
A karin bayanin da ya aika wa Legit, Sadiq Muhammad Maigatari ya bayyana cewa a ranar 23 ga watan Agusta, 2025, jami’an NDLEA da ke ƙarƙashin rundunar Kiru su ka kama matashin.
Ya kara da cewa sun kama shi a hanyar Zaria–Kano, a Kwanar Dangora, lokacin da yake dawowa daga jihar Legas tare da babban kwantena na ƙwayar Tramadol.
Ya ce an tabbatar cewa wanda ake zargin ya ɓoye ƙwayoyin Tramadol guda 7,000 masu nauyin kilo 4.1 a cikin jarkar mai mai lita 20, da nufin kau da hankali daga jami’an tsaro.
Duk da wannan dabara, a cewarsa, ƙwarewar jami’an NDLEA ta ba su damar gano kwayoyin cikin sauri, lamarin da ya nuna ƙwarewa da jajircewarsu wajen gano miyagun ƙwayoyi da aka ɓoye.
Hukumar NDLEA ta nemi daukin mazauna Kano
Kwamandan rundunar NDLEA a Kano, ACGN AI Ahmad, ya jinjinawa jami’an da suka gudanar da samamen bisa kwazo da ƙwarewa da suka nuna.
Ya kuma gode wa shugaban hukumar NDLEA na ƙasa, Manjo Janar Mohamed Buba Marwa (Rtd), bisa kulawa da goyon baya da yake bayarwa don yaki da ta'ammali da kwaya.

Source: Facebook
A kalaman kakakin hukumar, Sadiq Muhammad, ya ce:
"Babu shakka shigowar wannan kwaya jihar Kano ba karamin illa zai haifar b. Domin aba ce da take taba kwakwalwa kai tsaye. Aba ce da za ta lalaba kwakwalwar matasanmu, ta kum lalata mana al'umma."
Ya roki jama'a da su rika hakuri idan ana bincike a shingayen da aka samar a hanyoyi, domin ta nan ne ake iya gano bata gari har a zare su daga cikin matafiya.
NDLEA ta kama dillalan kwaya a Kano
A wani labarin, mun wallafa cewa Hukumar NDLEA ta reshen Kano ta bayyana cewa ta kama wani matashi mai suna Umar Adamu-Umar, mai shekaru 27, yana dauke da kilo 9 na wiwi.

Kara karanta wannan
'Da 'yar matsala,' An fara magana kan bai wa fursunoni damar yin zabe daga magarkama
Hukumar ta tabbatar da cewa an kama shi ne ranar 6 ga watan Agusta, 2025, a kan hanyar Zariya–Kano, inda jami’an NDLEA na rundunar Kiru suka yi masa samame yankin.
A cewar kakakin NDLEA, Sadiq Muhammad-Maigatari, wanda ya fitar da sanarwar, jami’an hukumar sun dade suna sa ido kan mai ake zargin kafin a cafke shi a hanyar dawowa daga Legas.
Asali: Legit.ng
