"Mafi Muni a Tarihin Najeriya": Obasanjo Ya Hada Buhari da Tinubu Ya Yi Musu Saukale
- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya sake caccakar gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari
- Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa gwamnatin farar hula ta Buhari, ita ce mafi muni da aka taba yi a tarihin Najeriya
- Hakazalika, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kamo hanyar gazawa kamar wadda ta gabace ta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya caccaki gwamnatocin marigayi Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Tinubu.
Olusegun Obasanjo ya bayyana mulkin marigayi Muhammadu Buhari a matsayin gwamnatin farar hula mafi muni a tarihin Najeriya.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta rahoto cewa tsohon shugaban kasan ya bayyana hakan ne a cikin sabon littafinsa mai suna “Nigeria: Past and Future”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Obasanjo ya ce kan Buhari?
Obasanjo ya tuna yadda Buhari ya yi amfani da zargin cewa gwamnatin marigayi Shehu Shagari ta lalace kuma ba ta da shugabanci mai kyau domin kafa hujjar kifar da ita.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya kadu da Allah ya yiwa tsohon gwamna kuma jigon APC rasuwa a Abuja
Ya kara da cewa, a lokacin, Buhari ya zargi ‘yan majalisar dokokin Jamhuriya ta biyu da gazawa wajen aiwatar da ayyukan kundin tsarin mulki, inda ya ce sun fi mai da hankali kan alawus.
Ya ce ya zarge su da neman karin fa’idodi da kuma tafiye-tafiye zuwa kasashen waje marasa amfani, ba tare da kula da tattalin arzikin kasa da walwalar jama’ar da suke wakilta ba.
Obasanjo ya yi mamakin yadda Buhari ya gaza magance waɗannan matsalolin bayan ya hau mulki a matsayin shugaban kasa, inda ya kara da cewa abubuwan da ya kamata a yi an bar su ba a yi ba.
"Kyakkyawan bayanin da Buhari ya gabatar lokacin da ya kifar da Shagari bai aiwatar da shi ba, bayan da ya zama shugaban kasa shekaru daga baya."
"Magana dai mai sauki ce, amma abubuwan da suka wajaba a yi an bar su ba a yi ba a lokacin gwamnatin farar hula ta Buhari daga 2015 zuwa 2023, gwamnatin farar hula mafi muni a tarihin Najeriya."
"Wataƙila wadannan tunani da kalaman ba nasa ba ne; kawai ya karanta abin da aka rubuta masa ne."
- Olusegun Obasanjo

Source: Twitter
Obasanjo ya caccaki gwamnatin Tinubu
Olusegun Obasanjo ya kuma bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana fafatawa da ta Buhari wajen gazawa.
Ko da yake bai yi tsokaci sosai kan dalilansa ba, tsohon shugaban kasan ya bayyana cewa:
"Gwamnatin Bola Tinubu ce kaɗai a yanzu da ake iya cewa tana fafatawa da ta Buhari (a wajen gazawa)."
Buhari ya hana tazarcen Obasanjo a 2006
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban hukumar VON, Osita Okechukwu, ya tuna baya kan yadda marigayi Muhammadu Buhari, ya kawo cikas ga tazarcen Olusegun Obasanjo a shekarar 2006.
Osita Okechukwu ya bayyana cewa Buhari ya tsaya tsayin daka wajen ganin cewa Obasanjo bai samu yadda yake so ba, wajen yin tazarce karo na uku.
Ya bayyana cewa Buhari ya rika yin tarurruka da shugabannin majalisa domin ganin cewa an yi fatali da burin na Obasanjo.
Asali: Legit.ng
