Kwale Kwale Ya Kife da Mutanen da Ke Tserewa Harin 'Yan Bindiga a Sokoto

Kwale Kwale Ya Kife da Mutanen da Ke Tserewa Harin 'Yan Bindiga a Sokoto

  • Wani jirgin ruwa na kwale-kwale ya gamu da hatsari a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Mutanen da ke cikin jrgin kwale-kwalen dai na tserewa 'yan bindiga ne bayan sun hango su suna kusanto inda suke
  • Hatsarin ya jawo an rasa rayukan mutane shida har lahira, yayin da wasu kuma aka nemesu aka rasa a cikin ruwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Akalla mutum shida sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum uku suka bace, sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya faru a yankin Garin Faji, karamar hukumar Sabon Birni, jhar Sokoto.

Hatsarin ya auku ne lokacin da mazauna yankin ke tserewa daga harin da ake zargin ‘yan bindiga sun kawo.

Jirgin ruwa ya kife da mutane a Sokoto
Hoton gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto Hoto: @ahmedaliyuskt
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mummunan lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Alhamis, 21 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

Mutane sun kama wata baiwar Allah bisa kuskuren zargi, sun kashe ta a tsakiyar kasuwa

Hatsarin jirgin ruwan shi ne karo na biyu da irin hakan ke faruwa cikin kasa da sati guda a jihar Sokoto.

Kwana shida kafin wannan lokaci, mutane hudu sun mutu a wani irin hatsari makamancin haka a ƙaramar hukumar Goronyo.

Mutane sun yi yunkurin tserewa 'yan bindiga

Waɗanda suka rasu sun kasance cikin jerin mazauna yankin da suka yi amfani da hanyar ruwa domin tserewa bayan sun hango ‘yan bindiga na kusantowa gare su.

Wani mazaunin yankin da ya yi magana cikin sirri ya bayyana cewa mutanen garin sun saba kwana a cikin dazuzzuka domin gujewa hare-haren dare, kuma yayin dawowarsu gidajensu ne hatsarin ya auku.

"Saboda tsoro, da yawa daga cikin mutane ba sa kwana a gidajensu. Da wannan safiyar, suna dawowa gida, sai kwale-kwalen ya kife.”

- Wata majiya

Wani mazauni kuma ya bayyana cewa firgici ya barke ne lokacin da mutanen suka hango ‘yan bindigan na kusantowa, abin da ya tilasta musu yin gaggawar tserewa ta ruwa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Plateau, an kashe mutane tare da bankawa gidaje wuta

'Yan bindga sun addabi mutane a Sokoto

Ɗan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar Sabon Birni, Hon. Aminu Boza, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Jirgin ruwa ya yi hatsari a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya bayyana cewa matsalar tsaro ta tilasta wa mutane da dama barin gidajensu.

"Wasu al’ummomi yanzu sun zama kango, babu kowa. Mafi yawan maza suna kwana a daji, sai da safe suke dawowa gida.”

- Hon. Aminu Boza

Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta tura motocin yaki masu sulke zuwa Sabon Birni domin ƙarfafa tsaro, kuma hakan ya samar da nasarori a wasu wurare.

'Yan bindiga sun kona mutane a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Katsina.

'Yan bindigan marasa imani sun kona mutane 20 bayan sun kai farmaki a wani kauye da ke cikin karamar hukumar Malumfashi.

Dan majalisar da ke wakiltar Malumfashi a majalisar dokokin jihar Katsina, Aminu Ibrahim, ya koka da cewa mutanen mazabarsa na rayuwa cikin firgici sakamakon hare-haren 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng