'Da 'Yar Matsala,' An Fara Magana kan Bai wa Fursunoni Damar Yin Zabe Daga Magarkama
Tun bayan da hukumar INEC ta ce tana aiki don tabbatar da cewa fursunoni za su samu damar kada kuri’a a zabubbukan gaba a Najeriya, aka fara samun ra’ayoyi daban-daban a kan batun.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – A baya, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hankalinsu ya karkarta wajen tabbatar fursunoni sun yi zabe kamar yadda doka ta tanada.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi Baftan Janar na Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS), Sylvester Nwacuche, a ziyarar ban-girma a hedikwatar hukumar a Abuja.

Source: Facebook
Voice of Nigeria ta wallafa cewa Farfesa Mahmood ya ce, hakkin kada kuri’a hakki ne na ɗan adam wanda bai kamata a hana kowanne ɗan ƙasa ba, ciki har da waɗanda ke cikin gidajen gyaran hali.
Ya ce hukumar ta san da hukuncin Babbar Kotun Tarayya a Benin da aka yanke ranar 16 ga Disamba 2014, da kuma na Kotun Ɗaukaka Kara a Benin ranar 7 ga Disamba 2018.
Waɗannan hukunce hukunce sun tabbatar da haƙƙin wasu mutane biyar da ke jiran shari’a na kada kuri’a a zabe.
Yadda ake zabe a gidajen gyaran hali
A zantawarsa da Legit, Kakakin gidan gyaran hali na jihar Kano, SCC Musubahu Kofar Nasarawa, ya shaida wa Legit cewa yin zabe a gidajen yari ba sabon abu ba ne.
Ya bayyana cewa tun da dadewa ake gudanar da zabe a gidajen gyaran hali, domin su ma fursunonin ‘yan ƙasa ne masu cikakken ‘yanci.
A SCC Musubahu Kofar Nasarawa:
“Ai dama can mazauna gidajen ajiya da gyaran hali suna yin zabuka, ana yin zabe kamar yadda ake yi a waje. Daga baya ne aka dakatar da hakan.

Kara karanta wannan
Jami'an NDLEA sun cafke dillalin miyagun kwayoyi da aka dade ana sa ido kansa a Kano
“Kuma ko a nan jihar Kano, ina ji a zaben farko wanda aka yi a Kurmawa, shi ne na gidan ajiya da gyaran hali. Haka zalika a Gwauron Dutse, shi ma na farko ne na gidan ajiya da gyaran hali. Saboda haka ana zabe.”

Source: Twitter
SCC Musubahu ya ƙara da cewa hukumar ta tabbatar da cewa zabe a gidajen ajiya zai yiwu, kuma ya dace a bai wa fursunoni dama kamar yadda dokar ƙasa ta tanada.
Ya ce abin da hukumar ke ƙara neman a fahimta shi ne cewa waɗanda ke jiran shari’a suna da ‘yancinsu, wato su ma ‘yan ƙasa ne.
‘Bai dace ba,’ in ji Ambasada Nasiru
Ambasada Nasiru Isah, tsohon Mataimakin Shugaban gidan gyaran hali mai ritaya, ya shaida wa Legit cewa ko da yake ci gaba ne sosai, amma idan aka duba daga wani ɓangare, abu ne da bai dace ba.
Ya ce idan aka dawo da gudanar da zabe a gidajen gyaran hali, to an bi dokar ƙasa tare da mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya.
A kalamansa:
“Dokar ƙasa ba ta ce don an daure ka ko an kai ka gidan yari, to baka da yanci ka zaɓi mutumin da kake ganin ya dace ya mulke ka ba. Wataƙila mulkin da ake yi maka shi ne baka ji daɗi ba, har ya sa ka aikata laifi.”
Ya ƙara da cewa:
“To yanzu ga dama, an ce ka zo ka zaɓi wanda kake ganin zai yi maka mulki, to kai ka zaɓa da kanka. Wataƙila idan ya zaɓi mai kyau, zai ba shi abin da yake so.”
Ambasada Nasiru ya ce barin yin zabe a kurkuku zai iya rage laifuffuka idan aka gudanar da sahihin zabe wanda zai bai wa fursunoni damar zaɓar shugaba nagari.
Ya ce kurkuku wata duniyar kanta ce, inda ake sanya mutum a takunkumi, kuma hakan zai iya rage yunƙurin ballewa daga gidajen yari kamar yadda ake fama da shi a wasu sassan ƙasar nan.
Zabe a kurkuku zai iya dagula lissafi
Ambasada Nasiru ya ce duk da kyawun tsarin, zai iya jawo wa gwamnatin Najeriya asara mai yawa, saboda gidan yari ba wurin zama na dindindin ba ne.
Ya ƙara da cewa akwai fursunoni da ke jiran shari’a waɗanda za a iya sakinsu bayan gajeren lokaci, da kuma waɗanda aka yankewa hukunci na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu
A cewarsa:
“Idan har kuka ce za a riƙa yi wa fursunoni rajista su yi zabe a cikin gidan yari, to wani ba zai yi wata ɗaya ba a sake shi, wani kuma ba zai yi wata biyu ba a sake shi. To idan aka sake shi, ya fita waje, wata kuri’a kuma zai yi kenan?
“Idan haka ta kasance, yana nufin mutum guda zai yi kuri’a sau biyu. Ko kuma ma ya rasa gaba ɗaya. Ba mutum guda ba ne kawai, dubban mutane ne hakan zai shafa.”
Ya ce sai dai idan gwamnati ta ware waɗanda aka yankewa hukuncin shekaru masu yawa a matsayin masu damar yin zabe a gidajen gyaran hali.
Ya kara da cewa akwai wadanda aka daure su a wasu jihohin da ba nasu ba, kuma ko da sun fita, a bari su rika dawo wa domin zabe zai kawo matsalar tsaro sosai.
Daurarre ya lashe zabe
A baya, mun wallafa cewa hukumar INEC ta ayyana Bright Emeka Ngene na LP a matsayin wanda ya lashe kujerar ɗan majalisar dokokin jihar Enugu mai wakiltar mazabar Enugu ta Kudu I.
Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin mai magana da yawun hukumar, Sam Olumekun, a wata takarda da aka fitar ranar Talata, 19 ga Agusta, 2025 duk da Bright na zaman gidan yari.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa an sake gudanar da zaɓen mazabar ne bisa umarnin kotu a ranar 16 ga watan Agusta.
Asali: Legit.ng


