Zulum Ya Yi Martani kan Zargin Sowore game da Abin da Ke Faruwa a Borno

Zulum Ya Yi Martani kan Zargin Sowore game da Abin da Ke Faruwa a Borno

  • Gwamna Babagana Zulum ya karyata zargin Omoyele Sowore da ya yi zarge-zarge kan gwamnatin jihar Borno
  • Sowore ya yi ikirarin cewa an kashe biliyoyin kuɗi kan tubabbun yan Boko Haram yayin da matasa ke tsare ba bisa ka’ida ba
  • Kakakin Zulum ya bayyana cewa shirin DRR yana taimaka wa waɗanda rikici ya shafa, ba wai kawai ga tsofaffin ’yan Boko Haram ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya mayar da martani game da zarge-zargen Omoyele Sowore.

Gwamnan ya karyata zarge-zargen da Sowore ya yi masa kan amfani da biliyoyi wajen inganta tubabbun tsofaffin ’yan Boko Haram.

Zulum ya yi martani ga Sowore
Zulum ya ƙaryata zargin da Sowore ke yi masa. Hoto: Professor Babagana Umara Zulum, Omoyele Sowore.
Source: Facebook

Kakakin Zulum, Abdulrahman Bundi, ya ce babu wani ɗakin azabtarwa da ake cewa ana tsare mutane, cewar Punch

Kara karanta wannan

Obasanjo ya kara rubuta littafi, ya fallasa aika aikar alkalai a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma ƙaryata ikirarin cewa yana da wani ɗakin azabtarwa da ake tsare wadanda suka yi zanga-zangar #EndBadGovernance sama da shekara guda.

Zarge-zarge da Zulum ya yi a Borno

Sowore ya rubuta a shafukan sada zumunta cewa Gwamna Zulum yana gudanar da ɗakin azabtarwa da ake kira “The Crack FC” a Maiduguri.

A cewarsa, an tsare wasu matasa da suka yi zanga-zangar #EndBadGovernance a wannan wuri tsawon shekara guda.

Haka kuma ya zargi gwamnan da tsare ƙananan yara kan shiga zanga-zanga, yayin da ake ware biliyoyin kuɗi ga tubabbun yan Boko Haram.

A wani rubutu a Facebook, Sowore ya bayyana cewa abin kunya ne yadda ake ba tsofaffin ’yan Boko Haram tallafi, amma matasa da ke neman shugabanci nagari ake tsarewa.

Gwamnatin Borno ta soki Sowore da ya zargi Zulum
Zulum ya kalubalanci Sowore kan zarge-zargensa. Hoto: Professor Babagana Umara Zulum.
Source: Facebook

Martanin Zulum game da zargin Sowore

Bundi ya bayyana cewa waɗannan zarge-zargen ba su da tushe, kuma an yi su ne domin yaudarar jama’a, ya ce zanga-zangar #EndBadGovernance ma ta shafi gwamnatin tarayya ne, ba gwamnatin Borno ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: 'Yan sanda sun cafke tsohon shugaban kasa kan zargin rashawa a Sri Lanka

Ya ƙara da cewa shirin DRR, wato sake tunani, gyara da dawo da tsofaffin yan Boko Haram yana da manufar taimaka wa waɗanda rikicin ya shafa.

Bundi ya bayyana cewa shirin DRR ba wai kawai ga tsofaffin ’yan ta’adda ne ake aiwatar da shi ba.

Ya ce mafi yawan kuɗaɗen shirin ana amfani da su wajen dawo da rayuwar waɗanda suka rasa komai a rikici.

Ya shawarci jama’a da su karanta takardun shirin DRR da aka wallafa a intanet don samun cikakken bayani.

A cewarsa, shirin DRR ya fi karkata wajen dawo da zaman lafiya da taimaka wa mutanen da aka azabtar da rikicin Boko Haram.

Gwamna Zukum ya yi garambawul a gwamnatinsa

Kun ki cewa Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi garambawul a gwamnatinsa domin kawo sauyi a cikinta.

Zulum ya sallami kwamishinoni biyu don farfado da shugabanci, ya yi godiya gare su tare da yi musu fatan alheri a gaba.

Sababbin kwamishinonin da aka nada su ne Injiniya Mohammed Habib da Ibrahim Hala Hassan, inda suka maye gurbin wadanda aka sauke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.