Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Wuta kan Maboyar 'Yan Bindigan da Suka Kashe Masallata a Katsina
- Rundunar sojojin saman Najeriya ta samu nasarar kai hare-hare masu zafi a maboyar 'yan bindiga da ke jihar Katsina
- An kai hare-haren ne a maboyar 'yan bindigan da suka kai mummunan hari kan masallata a karamar hukumar Malumfashi
- Sojojin rundunar sun samu nasarar ceto mutane maau yawa da 'yan bindigan suka yi garkuwa da su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Rundunar sojojin saman Najeriya ta kai wani farmakin sama na musamman kan maboyar wani fitaccen jagoran ’yan bindiga a Katsina.
Dakarun sojojin rundunar sun kuma ceto mutane 76 da aka yi garkuwa da su, ciki har da mata da yara.

Source: Getty Images
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Nasir Mu’azu, ya fitar a ranar Asabar, 23 ga watan Agustan 2025, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kai samame kan maboyar 'yan bindiga
Kwamishinan ya bayyana cewa an kai samamen ne a maboyar wani jagoran ’yan bindiga mai suna Babaro da tawagarsa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Ya ce su ne ke da alhakin mummunan harin da aka kai kwanan nan a Gidan Mantau, cikin karamar hukumar Malumfashi, inda aka kashe masallata.
"Da safiyar yau rundunar sojojin saman Najeriya ta kai wani gagarumin farmaki a Tsaunin Pauwa, cikin karamar hukumar Kankara, inda aka yi nasarar ceto mutane 76 da aka yi garkuwa da su, ciki har da mata da yara."
"Wannan harin da aka kai tsakanin karfe 6:00 zuwa 7:00, an kai shi ne a maboyar Babaro da ke tsaunin Pauwa, wadda ta dade tana zama wata fitacciyar mafakar ’yan bindiga da ke addabar al’ummomin da ke kewaye."
- Nasir Mu'azu
Sojojin sama sun ceto mutane a Katsina
Nasir Mu’azu ya tabbatar da cewa dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su a lokacin harin Gidan Mantau na cikin waɗanda aka ceto.
Sai dai kuma ya bayyana bakin cikin cewa wani yaro ɗaya ya rasa ransa a yayin wannan farmakin.
Ya bayyana samamen a matsayin babban ci gaba a kokarin samar tsaro da ake yi a fadin jihar Katsina.

Source: Facebook
Ya kara da cewa matakin wani ɓangare ne na shirin da aka tsara don rushe maboyar ’yan ta’adda, karya su da kawo karshen kashe-kashe, garkuwa da mutane da suke yi wa jama’a.
Gwamnatin jihar Katsina ta jinjinawa rundunar sojojin saman Najeriya, rundunar sojojin kasa, da sauran jami’an tsaro bisa jarumta da kwarewarsu.
"Mun tsaya tsayin-daka wajen tallafa musu ta fuskar kayan aiki, musayar bayanan sirri, har sai an kawar da ’yan bindiga baki ɗaya."
- Nasir Mu'azu
Muhammad Mika ya nuna jin dadinsa kan yadda dakarun sojojin suka samu nasarar ceto mutanen da aka sace.
"Sun yi kokari sosai kuma sun cancanci a yaba musu. Muna yi musu fatan Allah ya ci gaba da ba su nasara kan miyagu."
"Matsalar rashin tsaron nan ta wuce duk yadda ake tunani, akwai tashin hankali kan yadda abubuwa suka tabarbare."
- Muhammad Mika
Sojoji sun kashe kwamandojin Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin sama na rundunar Operation Hadin Kai, sun samu nasarar kashe kwamandojin kungiyar Boko Haram.
Sojoji sun kashe kwamandoji biyu tare da wasu mayakan Boko Haram guda 11 bayan sun yi yunkurin kai hari a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.
Dakarun sojojin sun kuma kwato makamai masu tarin yawa da suk hada da bindigogi da alburusai daga hannun miyagun 'yan ta'addan.
Asali: Legit.ng


