Jerin Sunaye: Mutane 17 Yan Gidan Sarauta Sun Fara Neman Karagar Sarki bayan Ya Rasu

Jerin Sunaye: Mutane 17 Yan Gidan Sarauta Sun Fara Neman Karagar Sarki bayan Ya Rasu

  • Shirin nada magajin Sarkin Ijebu da ke jihar Ogun ya dauki dumi yayin da aka samu yan takara 17 da suka nuna sha'awa
  • Hakan dai na zuwa ne bayan rasuwar Sarkin Ijebuland, Oba Sikiru Kayode Adetona, wanda Allah ya karbi ransa ranar 13 ga watan Yuli, 2025
  • Rahotanni daga gidan Fusengbuwa sun nuna cewa zuwa yanzu akalla mutane 17 ne suka nuna sha'awa amma dole sai an bi matakan doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - An fara fafutukar neman wanda zai gaji sarautar Sarkin Ijebuland bayan rasuwar mai martaba Oba Sikiru Kayode Adetona, Ogbagba II.

Mai Martaba Sarkin wanda ke jihar Ogun, ya rasu da yammacin Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, yana da shekaru 91.

Sarkin Ijebu, Oba Sikiru.
Marigayi Awujalen na Ijebuland, Oba Sikiru Kayode Adetona Hoto: Kayode Adetona
Source: UGC

Yadda aka yi jan'izar Sarkin Ijebu a Ogun

Kara karanta wannan

'An bar Arewa a baya,' Remi Tinubu za ta bude kamfani a Legas, an fara korafi

Jaridar Leadership ta tattaro cewa an yi jana'izarsa tare da birne ne shi kamar yadda addinin musulunci ya tanada washegari, sannan aka yi zaman makoki a Ijebu-Ode.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin shi ne mafi dadewa a sarautar Awujale a tarihin masarautar, inda ya hau gadon sarauta tun daga shekarar 1960 har zuwa rasuwarsa.

Oba Adetona ya fito ne daga tsatson gidan Anikinaiya kuma ya shahara wajen kare al’adun gargajiya da ci gaban yankinsa.

Wane gida zai fitar da sabon Sarkin Ijebu

A bisa tsarin doka ta Chiefs Law 1957 da ta tanadi yadda ake zaben sabon Awujale, akwai gidajen sarauta guda hudu da ke karba-karba wajen samar da Sarki.

Gidajen sun hada da gidan Gbelegbuwa, gidan Anikinaiya, gidan Fusengbuwa, da gidan Fidipote. Wannan tsarin an amince da shi tun a 1959, kafin Marigayi Sarki Adetona ya hau mulki.

A wannan karon, gidan Fusengbuwa ne ya kamata ya fitar da sabon Sarki, kuma zuwa yanzu, sama da mutum 17 sun bayyana sha’awar gaje sarautar.

Jerin wadanda ke neman zama Sarki a Ijebu

Wadanda suka nuna sha'awar kujerar Sarkin sun hada da:

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Sarki mai martaba a Najeriya ya rasu yana mai shekaru 89

1. Prince Adewale Alausa

2. Prince Ademola Aderibigbe

3. Prince Taiwo Otun

4. Hon. Olaseni Otun

5. Otunba Sakiru Bello

6. Prince Olawale Yusuf Oriola

7. Prince Adeleke Adeyemi Akeem

8. Prince Adekunle Agbasale

9. Prince Adewale Adekoya Ayodele

10. Otunba Fatai Arowolo

11. Prince Adeleye Lateef

12. Prince Adewale Akeem Adeleke

13. Prince Adeyemi Oduwole

14. Prince Onabanjo Oladayo

15. Prince Odunowo Adebowale Emmanuel

16. Prince Adegbenro Bello,

17. Prince Adewale Ayoola Olasupo Bello.

Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun.
Hoton gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun a ofishinsa Hoto: Prince Dapo Abiodun
Source: Facebook

Matakan da za a bi wajen nadin Sarkin Ijebu

Sai dai kafin a zabi sabon Sarki, akwai tsauraran matakan gargajiya da na doka da za a bi.

Masu zaben Sarkin za su tantance kafin tsayar da sunan wanda zai gaji sarauta, sannan sai Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya amince da zabin kafin nada shi a hukumance.

Za a nada sabon Sarkin Ibadan, Rashidi Ladoja

A wani labarin, kun ji cewa an shirya bikin nadin tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja a matsayin sabon Sarkin Ibadan watau Olubadan na 44.

Kara karanta wannan

Nijar: An harbe shugaban Boko Haram da ya maye gurbin Shekau har lahira

Bayanai sun nuna cewa za a naɗa Rashidi Ladoja a matsayin Olubadan na 44 na Ibadan, ranar Juma'a 26 ga watan Satumba, 2025.

An tattaro cewa tuni tawagar gwamnatin jihar Oyo ta gana da Ladoja da sauran mambobin majalisar masarautar a gidansa da ke Bodija.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262