Hafsan Hafsoshi Ya Bukaci 'Yan Najeriya Su Dauki Makamai? Hedkwatar Tsaro Ta Yi Bayani

Hafsan Hafsoshi Ya Bukaci 'Yan Najeriya Su Dauki Makamai? Hedkwatar Tsaro Ta Yi Bayani

  • Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta fito ta warware zare da abawa kan batun cewa Janar Christopher Musa, ya bukaci jama'a su dauki makamai
  • DHQ ta bayyana cewa an sauya kalaman da babban hafsan hafsoshin ya yi ne kan batun kare kai
  • Ta nuna cewa Janar Christopher Musa, shawara ya ba da ga 'yan Najeriya kan hanyoyin da za su tsira da ransu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta yi magana kan batun cewa babban hafsan hafsoshi, Janar Christopher Musa, ya yi kira ga 'yan Najeriya su mallaki makamai.

DHQ ta bayyana cewa Janar Christopher Musa, bai taɓa yin kira ga ’yan kasa, su dauki makamai ko kuma su shiga mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Hedkwatar tsaro ta kare babban hafsan hafsoshi
Babban hafsan hafsoshi, Janar Christopher Musa, a wajen wani taro Hoto: @DefenceInfoNg
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na hedkwatar tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya fitar a ranar Juma'a, 22 ga watan Agustan 2025, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An fadi sojojin da suka fi yan bindiga hatsari, an nemo mafita

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin wata hira da aka yi da shi a ranar Alhamis, Janar Christopher Musa ya bayyana cewa ’yan Najeriya su koyi dabarun tsira da kuma fasahohin kare kai, a matsayin hanya ta tsira a wuraren da ke da rashin tsaro.

DHQ ta fayyace kalaman hafsan hafsoshi

Birgediya Janar Tukur Gusau, ya bayyana cewa babban hafsan bai nufin yin kira ga mutane su ɗauki makamai ba, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Ya ce sai dai ya karfafa gwiwar ’yan Najeriya wajen koyon dabarun tsira da kariyar kai irin su tuki, iyo, taekwondo, judo da kuma dambe.

"Hedikwatar Tsaro ta lura cike da damuwa game da kokarin da wasu ke yi na ɓata fassarar maganganun babban hafsan hafsoshi, Janar Christopher Gwabin Musa, a lokacin hirarsa da Channels Tv da yammacin ranar Alhamis 20 ga watan Agusta, 2025.”
"A cikin wannan hira, CDS ya karfafa ’yan Najeriya su kara samun hanyoyin tsira da dabarun kare kai, inda ya kwatanta irin wannan horo da abubuwan da aka amince da su irin su tuki, taekwondo, judo, iyo, dambe da sauransu."

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An gano yadda ake amfani da siyasa wajen zafafa hare hare a Najeriya

"Domin kawar da duk wani ruɗani, CDS bai kira ’yan ƙasa da su ɗauki makamai ko su shiga cikin mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba."
"Yana sane da dokokin Najeriya da ke hana ɗaukar makamai ba tare da izini ba. Sakonsa shi ne na karrfafa juriya, sanin makamar aiki a kowanne yanayi, da kuma shirin tsaro bisa ka’ida, ba don karfafa wani aiki na haramtacciyar hanya ba."

- Birgediya Janar Tukur Gusau

Hedkwatar tsaro ta yi magana kan kalaman hafsan hafsoshi
Hoton babban hafsan hafsoshi, Janar Christopher Gwabin Musa Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Dakarun Sojoji na samun nasara kan 'yan ta'adda

Birgediya Janar Tukur Gusau ya kara da cewa rundunonin sojojin Najeriya tare da sauran hukumomin tsaro na samun nasarori a ci gaba da ayyukan da suke gudanarwa kan matsalar tsaro.

Ya ba da tabbacin cewa tsaron ’yan ƙasa shi ne babban fifikon da suka sanya a gaba.

Sojoji sun kashe kwamandojin Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka Kwamandojin Boko Haram guda biyu a Borno.

Sojojin na rundunar Operation Hadin Kai sun kuma kashe waau mayakan kungiyar guda 11 bayan sun yi yunkurin kai wani hari.

Hakazalika, sun kuma kwato tarin makamai da suka hada da bindigogi da alburusai daga hannun 'yan ta'addan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng