'Ku Ji da Kyau': Yahaya Bello Ya ba Ƴan Majalisun Kogi Umarni game da Gwamna Ododo
- An yaɗa wani faifan bidiyo da aka gano tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, yana ba yan majalisar dokokin jiharsa umarni
- Yahaya Bello ya bukaci 'yan majalisar dokoki su mara wa Gwamna Usman Ododo baya, domin ci gaban jihar gaba ɗaya
- A bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, Bello ya umarci manyan mutanen su zauna ƙasa, hakan ya jawo sukar jama'a
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lokoja, Kogi - Wani bidiyon tsohon gwamnan Kogi da yan majalisu ya jawo maganganu a kafofin sadarwa.
An gano tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello yana ba mambobin majalisar umarni a wata ganawa da aka yi a gidansa da ke jihar Kogi.

Source: Facebook
A bidiyon da Daily Trust ta yada, Yahaya Bello ya bukaci mambobin majalisar dokoki na jihar da su mara wa gwamnatin Gwamna Usman Ododo baya.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An taso Yahaya Bello bayan barin gwamna
Bello, ya mika mulki ne ga Ahmed Usman Ododo bayan kammala wa’adinsa a watan Janairu 2024, wanda ya gaje shi domin ci gaba da mulkin jihar.
Tun bayan mika mulki ga Gwamna Ododo, an fara maganar tuhume-tuhume da ake yi kan Yahaya Bello na zargin badakalar makudan kudi.
Hukumar yaki da cin hanci ne ta EFCC fara tuhumar tsohon gwamnan kan zargin almundahana fiye da N80bn yayin da yake mulkin jihar.
Umarnin da Yahaya Bello ya ba yan majalisa
A cikin jawabin nasa ga ‘yan majalisar, tsohon gwamnan ya umarce su da su zauna a kasa, inda ya bukaci haɗin kansu a jihar.
Ya yi kira gare su da su yi aiki tare da Kakakin majalisar, Aliyu Umar Yusuf, da sauran mambobi wajen tallafa wa Gwamna Ododo.
Tsohon gwamnan ya jaddada bukatar majalisar ta goyi bayan duk wasu kudurori da gwamnatin Ododo za ta kawo gaban majalisar jihar Kogi.

Kara karanta wannan
Bayan dawowa daga London, Ganduje ya bi sawun Shettima da Zulum wajen ta'aziyya Kogi
Ya ce:
“Zauna a ƙasa, Don haka, yanzu da za ku shiga... Ku je ku ba da haɗin kai da Kakakin majalisar da sauran mambobi ku tallafa.
“Ku kasance cikin waɗanda za su goyi bayan Gwamna Ahmed Usman Ododo a duk abin da ya zo gaban majalisar."

Source: Twitter
Alakar da ke tsakanin Yahaya Bello, Ododo
Bayan wannan jawabi nasa, ‘yan majalisar sun yi tafi cikin murna a matsayin martani da godiya ga tsohon gwamnan bayan kammala jawabin nasa.
Hakan ya kara tabbatar da irin alaka mai kyau tsakanin Yahaya Bello da Gwamna Ahmed Usman Ododo a jihar wanda ba kasafai hakan ke faruwa ba.
Yahaya Bello ya auri mata ta 4
Mun ba ku labarin cewa an tabbatar da cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya angwance a bikin da aka gudanar a birnin tarayya, Abuja.
Yahaya Bello ya angwance ne a karo na hudu a Abuja da matarsa, Hiqma a wani bikin sirri da danginsa da abokai suka halarta wanda aka yi.
Matarsa ta uku, Hafiza, ta tabbatar da auren a kafar sadarwa, inda ta yi maraba da sabuwar amarya tare da addu’ar albarka da zaman lafiya.
Asali: Legit.ng