1447: Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa Ana Shirin Shiga Watan Maulidin Annabi SAW

1447: Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa Ana Shirin Shiga Watan Maulidin Annabi SAW

  • Sarkin Musulmi ya umarci a fara duban jinjirin watan Rabi'ul Awwal na 1447AH daga gobe Asabar, 29 ga watan Safar daidai da 23 ga watan Agusta, 2025
  • Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bukaci musulmi su kai rahoton ganin watan ga magajin gari ko hakimi domin isar da sakon ga masarautarsa
  • Watan Rabi'ul Awwal shi ne na uku a jerin watannin kalandar musulunci kuma a cikinsa ne aka haifi fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ba da umarnin fara duban jinjirin watan Rabi'ul Awwal a Najeriya

Sarkin Musulmi ya bayyana gobe Asabar, 23 ga watan Agusta, 2025 daidai da 29 ga watan Safar, 1447aH a matsayin ranar fara duban jinjirin watan Rabi'ul Awwal.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Sarki mai martaba a Najeriya ya rasu yana mai shekaru 89

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III.
Hoton Mai Alfarma Sarkin Musulmi,.Muhammad Sa'ad Abubakar III a wurin taro Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Getty Images

Punch ta rahoto cewa majalisar masarautar Sarkin Musulmi da ke Sakkwato ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar yau Juma'a.

Sanarwar ta fito ta hannun shugaban kwamitin kula da harkokin addini na masarautar Sarkin Musulmin Najeriya, Farfesa Sambo Junaidu, wanda shi ne wazirin Sakkwato.

Sarkin Musulmi ya bukaci a fara duba wata

Ya ce kamar yadda aka sani an ware ranar 29 ga kowane watan kalandar musulunci a matsayin ranar fara duban jinjirin wata mai kamawa.

Farfesa Sambo ya bukaci daukacin musulman Najeriya da su fita duban watan Rabi'ul Awwal daga gobe Asabar.

Sanarwar ta ce:

“Ana bukatar Musulmi da su duba jinjirin watan Rabi’ul Awwal a ranar Asabar, 29 ga watan Safar, 1447H kuma su kai rahoton ganin watan ga hakimin yankinsu ko magajin gari mafi kusa.
"Ta haka ne za a a isar da sakon ganin watan ga Mai Alfarma, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya.”

Kara karanta wannan

Mambobi 4 sun shiga matsala mai girma da suka yi yunkurin tsige kakakin majalisa

Sanarwar ta jaddada muhimmancin hada kai wajen cika wannan ibada, wadda take tabbatar da fara watan Rabi’ul Awwal, na uku a kalandar Musulunci.

Sarkin Musulmin Najeriya.
Hoton mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Getty Images

Ana shirin shiga watan Maulidi a Najeriya

Galibi dai an fi sanin watan Rabi'ul Awwal a matsayin watan haihuwar Annabi Muhammad (SAW), watan da wasu daga cikin masulmi ke yin Maulidi.

Farfesa Junaidu ya yi addu’ar neman jagorancin Allah wajen gudanar da wannan ibada, yana cewa: “Allah Madaukakin Sarki ya taimake mu a wannan aiki.”

Musulmi musamman mabiya darikar Tijjaniyya a Najeriya kan shirya tarurruka da dama su na murnar zagayowar watan da aka haifi fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (S.A.W).

Sarkin Musulmi ya yaba da nadin Olubadan

A baya, kun ji cewa Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya taya sabon Sarkin Ibadan, Alhaji Rashidi Ladoja murnar nadinsa.

Sarkin Musulmi ya yi farin ciki da nasarar da sabon sarkin ya samu, wanda zai gaji marigayi Oba Akinloye Owolabi Olakulehin da ya rasu a ranar Litinin, 7 ga Yuli, 2025.

Ya yabawa gwamnan bisa amincewa da zabin jama'a, yana mai cewa sabon Sarkin yana da gogewa a fannoni daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262