'Mun Sha Azaba,' Adadin Bayin Allah da 'yan Ta'adda Su Ka Hallaka a Katsina Ya Haura 55

'Mun Sha Azaba,' Adadin Bayin Allah da 'yan Ta'adda Su Ka Hallaka a Katsina Ya Haura 55

  • Mutanen Gidan Mantau a Malumfashi, jihar Katsina, sun bayyana irin halin ƙunci da suka shiga bayan mummunan harin ‘yan ta’adda a yankin
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa sama da gawarwaki 50 aka gano, yayin da ake ci gaba da binciken wasu a cikin dazuka
  • Mazauna yankin sun roƙi gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina da su ɗauki mataki don kare su daga ƙarin hare-hare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina Wadanda suka tsira daga mummunan harin da ‘yan ta’adda suka kai wa al’ummar Gidan Mantau a karamar hukumar Malumfashi, jihar Katsina a ranar Talata, sun bayyana irin azabar da suka sha.

Mutanen garin sun gano gawarwakin mutane fiye da 55, kuma har yanzu suna ci gaba da neman wasu a cikin daji.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Plateau, an kashe mutane tare da bankawa gidaje wuta

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda
Hoton gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda Hoto: Dr. Umaru Dikko Radda
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mazauna yankin sun roƙi gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina su kawo dauki domin kubutar da su daga ci gaba da hare-hare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan ta’adda sun yi barna jihar Katsina

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa duk da an kai kusan kwanaki uku bayan harin, har yanzu babu cikakken bayani a kan irin barna da aka yi a Gidan Mantau.

Rahotanni sun ce akwai barazana a yankin wanda ya hana jami’an gwamnati da masu aikin ceto shiga, yayin da mazauna suka ci gaba da zama a cikin dardar.

Wadanda suka tsira sun bayyana cewa jami’an gwamnatin jihar Katsina sun ɗauki lokaci mai tsawo kafin su iso yankin.

Taswirar jihar Katsina
Taswirar jihar Katsina Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rahotanni sun ce jami'an sun tsaya a bakin hanya suka yi magana da shugabannin al’umma da mutanen da abin ya rutsa da su.

Haka kuma, an gano cewa iyalai da dama da ba su ga gawar ‘yan uwansu ba yanzu suna ci gaba da bincike a dazuzzuka da taimakon abokai.

Kara karanta wannan

'Akwai matsala a N70, 000,' Amurka ta fitar da rahoto kan mafi karancin albashin Najeriya

Mutane sun tabbatar da cewa adadin waɗanda suka mutu ya kai 55, sama da alkaluman 34 da hukumomi suka tabbatar.

Yadda ‘yan ta’adda ke kai hari a Katsina

Mazauna kauyen na Katsina sun bayyana cewa kusan shekara guda da ta gabata ma, ‘yan ta’adda sun kashe mutum fiye da 20 a irin wannan hari.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban rundunar tsaro, Janar Christopher Musa, ya nuna damuwarsa kan sake tashi tashin hankali a Katsina da wasu sassan Arewa.

Janar Musa ya ce rundunar soji ta ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukan tsaro a faɗin ƙasar, sai dai ya amince cewa kashe-kashen na tayar da hankali.

Rahoton ya bayyana cewa ƙungiyar ta’addan da ake zargi da kisan na baya-bayan nan tana ƙarƙashin jagorancin sanannen shugaban ‘yan ta’adda, Mustapha Babaro.

Babaro na gudanar da ayyukansa a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina da kuma wasu yankunan jihar Zamfara.

An gano cewa bayan da suka kai hari kan masallaci, ‘yan ta’addan sun yi yawo a kauyen suna kashe mutane da kuma yin garkuwa da wasu.

Kara karanta wannan

Duk da yin sulhu, 'yan bindiga sun kashe manoma a Kaduna

'Yan ta'adda sun gindaya sharadi a Katsina

A baya, mun wallafa cewa 'yan bindiga sun kakaba harajin Naira miliyan 15 ga mutanen garuruwan da ke karkashin gundumar Almu a karamar hukumar Malumfashi.

Wannan na zuwa ne bayan harin kisa da aka kai a masallaci, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane har 55 kuma har yanzu ana ci gaba da zakulo gawarwakin jama'a.

A cewar Kansilan Gundumar Almu, Usman Usman, ‘yan ta’addan sun buƙaci Naira miliyan 10 da kuma babura Honda guda biyu daga garuruwa kimanin takwas zuwa tara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng