Daga Japan, Tinubu Ya Lula zuwa Kasar Brazil, An Fadi Lokacin Dawowarsa Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu ya tashi daga Yokohama, Japan, zuwa Brazil inda zai fara ziyarar aiki ranar Lahadi, 24 ga watan Agusta
- A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, ya yi wata 'yar tsayawa a Los Angeles kafin ya nufi Brasília, babban birnin Brazil
- Wannan tafiya ta zama mataki na biyu a rangadin ƙasashen biyu da ya fara daga Abuja ranar 15 ga watan Agusta 2025
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Shugaba Bola Tinubu ya baro Yokohama, Japan, a daren Alhamis zuwa Brazil, inda zai fara ziyarar aiki a ranar Lahadi, 24 ga watan Agusta.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Mista Bayo Onanuga, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa, inda ya ce Tinubu zai biya ta Los Angeles kafin ya wuce Brasília, babban birnin Brazil.

Kara karanta wannan
Malamin addini ya yi hasashe kan tazarcen Tinubu, ya fadi sharadin da zai sa ya sha kaye

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce wannan tafiyar zuwa Brazil ita ce ta biyu daga cikin rangadin ƙasashen da Bola Tinubu ya fara tun daga Abuja a ranar 15 ga watan Agusta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya yada zango a birnin Dubai
The Nation ta wallafa cewa a hanyarsa zuwa Japan, shugaban kasa ya tsaya na ɗan lokaci a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa, kafin ya isa Yokohama da safiyar 18 ga watan Agusta.
Yayin da yake Japan, Tinubu ya halarci taron shugabanni na tara na ci gaban kasashen Afrika da aka gudanar a Tokyo (TICAD9), tare da halartar tattaunawa a ranar 20 ga watan Agusta.
Shugaban ya kuma gudanar da jerin tarukan haɗin gwiwa da jami’an gwamnatin Japan, shugabannin kasuwanci domin ƙarfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Japan.

Source: Facebook
Haka kuma, ya yi amfani da wannan ziyara wajen jaddada shirin gwamnatinsa na gyaran tattalin arziki da tallata Najeriya ga Japan a fannoni kamar gine-gine, fasaha da makamashin zamani.

Kara karanta wannan
'Dan APC ya firgita da hadaka, ya fadi yadda Atiku da Obi za su iya kifar da Tinubu
Baya ga harkokin gwamnati, Tinubu ya kammala ziyarar tasa da zaman tattaunawa da ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje a daren Alhamis a Yokohama.
A wurin taron, ya yaba da gudummawar su wajen ci gaban ƙasa tare da jaddada musu muhimmancin kasancewa jakadun ƙasa nagari, kana ya bukace su su zuba hannun jari a gida.
Me shugaba Tinubu zai yi a kasar Brazil?
A yayin da yake Brazil, Tinubu zai mayar da hankali kan harkokin kasuwanci, tsaro da musayar al’adu, domin ƙarfafa dangantakar Najeriya da babbar ƙasar Latin Amurka.
Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa tattaunawar za ta kuma shafi haɗin kai a fannin noma, sauya makamashi da tsaron yankin, wadanda suke da muhimmanci ga ƙasashen biyu.
Harkokin shugaban na Najeriya a Brazil za su haɗa da gana wa da shugaban ƙasar Luiz Inácio Lula da Silva da kuma wasu manyan jami’an gwamnati.
Haka kuma, ana sa ran zai gana da al’ummar Najeriya da ke Brazil don ya bayyana masu manufofin gwamnati da ƙarfafa rawar da suke takawa a ci gaban ƙasa.
Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa Tinubu zai dawo Najeriya bayan kammala dukkannin ayyukansa a Brazil.
Tinubu ya magantu kan rashin tsaro
A baya, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatin sa za ta magance matsalar rashin tsaro ta hanyar gano bakin zaren matsalar tun daga tushe ko jama'a sa sarara.
A jawabinsa na ranar Laraba, 20 ga Agusta, 2025, yayin taro kan zaman lafiya da dorewa a TICAD9 dake Yokohama, Japan, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa na aiki tukuru.
Ya ce gwamnatinsa da gaske ta ke yi, kuma tana son kawo karshen matsalar tsaro ne ta hanyar gano bakin zaren matsalar, wato tushen abin da ke haifar da ta’addanci da rashin tsaro.
Asali: Legit.ng
