Tinubu Ya Kawo Manhajar Lissafin Haraji da Kowa zai Duba Nawa zai Biya da Kansa

Tinubu Ya Kawo Manhajar Lissafin Haraji da Kowa zai Duba Nawa zai Biya da Kansa

  • Bola Tinubu ya ce sabuwar manhajar lissafin haraji za ta taimaka wa ‘yan Najeriya su fahimci yadda sabon tsarin haraji zai shafe su
  • An ƙaddamar da na’urar ne domin kwatanta tsakanin abin da ake biya a yanzu da kuma yadda za a biya daga Janairu 2026
  • Tinubu ya jaddada cewa tsarin zai kare marasa ƙarfi, ya kawar da nauyin haraji daga talakawa, tare da samar da daidaito da gaskiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da sabuwar manhajar lissafin haraji ga 'yan Najeriya.

Sabuwar manhajar za ta ba da damar auna yadda sabon tsarin harajin da gwamnatinsa ta amince da shi zai shafi kuɗin shiga na ‘yan ƙasa.

Shugaba Bola Tinubu yayin wata ziyara jihar Katsina
Shugaba Bola Tinubu yayin wata ziyara jihar Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Source: Twitter

Legit Hausa ta gano cewa shugaban ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a daren Juma'a.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An gano yadda ake amfani da siyasa wajen zafafa hare hare a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta bayyana cewa an samar da na’urar ne domin baiwa kowa damar kwatanta abin da yake biya a yanzu da kuma abin da zai biya daga shekarar 2026.

Tinubu ya ce manufar gyaran harajin ita ce tabbatar da tsarin adalci, wanda ba zai zame wa marasa galihu nauyi ba, sai dai ya tabbatar da rabon arziki da sauƙaƙe biyan haraji.

Tinubu ya kawo sabuwar manhajar haraji

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa manhajar za ta taimaka wa mutane wajen fahimtar tasirin sauye-sauyen da gwamnati ta kawo a tsarin biyan haraji.

Punch ta wallafa cewa ya ce:

“An samar da wannan na’ura ne domin auna sabon tsarin da tsohon, sannan a ga yadda ya shafi masu ƙaramin karfi.
"Wannan tsarin zai tabbatar da gaskiya, daidaito, da kuma sauƙin biyan haraji ga kowa.”

Manufofin gyaran haraji da Tinubu ke yi

A cewar shugaban ƙasar, sabon tsarin zai fara aiki ne daga watan Janairu 2026, kuma yana ɗauke da manufofi na kawar da nauyin haraji daga talakawa.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An gano sabuwar hanyar da ake daukar nauyin ta'addanci a Najeriya

Tinubu ya jaddada cewa tsarin haraji mai kyau bai kamata ya danne talaka ba, ko kuma ya ƙara wa marasa ƙarfi wahala.

Maimakon haka, ya ce an tsara shi ne domin ya ƙarfafa masu ƙaramin karfi tare da tabbatar da gaskiya a tattalin arzikin ƙasa.

Yadda za a yi aiki da manhajar harajin

Shugaban ya yi kira ga ‘yan Najeriya su gwada na’urar domin su ga daidai yadda gyaran zai shafe su.

Ya ƙara da cewa tsarin zai taimaka wajen kare masu ƙaramin kuɗi, samar da ingantaccen tsarin rabon arziki, da kuma sauƙaƙa biyan haraji ba tare da rikitarwa ba.

Duk wanda ya ke son shiga manhajar domin duba harajin da zai rika biya zai iya danna nan domin gwadawa.

Tinubu ya saka tallafin wankin koda

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kawo shirin tallafin wankin koda a jihohi.

Ma'aikatar lafiya ta kasa ta bayyana cewa an kawo shirin ne a asibitocin gwamnatin tarayya a jihohi 11 domin saukakawa talakawa.

Ministan lafiya ya bayyana cewa Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano na cikin wajen da aka tanada, sabanin masu cewa an ware Arewa ta Yamma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng