'Yan ADC Sun Fusata El Rufa'i saboda Kalaman Bogi kan Tinubu, Ya Gargadi Mutanensa

'Yan ADC Sun Fusata El Rufa'i saboda Kalaman Bogi kan Tinubu, Ya Gargadi Mutanensa

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya gargadi kungiyar ADC Vanguard da ta daina kirkirar magana da sunansa
  • Malam Nasir El-Rufa'i ya ce yana da shafukan sada zumunta na gaskiya da yake amfani da su wajen bayyana ra’ayinsa
  • An rahoto cewa kungiyar ta nemi afuwarsa bayan tsohon gwamnan ya nesanta kansa daga kalaman da aka danganta masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya fito fili ya yi watsi da kalaman da wata kungiya mai suna ADC Vanguard ta alakanta da shi a shafin sada zumunta.

El-Rufa'i ya bayyana cewa ya ba da gargadi kan wannan dabi’a domin tana iya cutar da jam’iyyar da suke mara wa baya.

El-Rufa;i na jawabi a wani taro da ya halarta
Malam El-Rufa'i na jawabi a wani taro da ya halarta. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Twitter

El-Rufai ya yi magana ne a X inda ya ce yana da shafukan sada zumunta na gaskiya inda yake bayyana duk wani ra’ayinsa, don haka bai ga dalilin da zai sa a kirkiri magana a sunansa ba.

Kara karanta wannan

Tsohon ministan Buhari ya yi magana game da mulki, 'yan adawa da halin da APC take ciki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan wannan martani, kungiyar ADC Vanguard ta fito ta nemi afuwa kan abin da ta yi, tare da alkawarin kaucewa irin wannan kuskure a nan gaba.

Nasir El-Rufai ya gargadi ADC Vanguard

A cikin sakonsa, El-Rufai ya yi kira ga kungiyar da ta daina danganta masa kalaman da bai taba furtawa ba.

Ya ce:

“Ina da shafukan sada zumunta na gaskiya inda nake bayyana ra’ayina. Don haka babu dalilin da zai sa a rika jingina min maganar da ban taba yi ba.”

Ya kara da cewa ko da kuwa ya amince da sakon da aka yada, zai nesanta kansa daga gare shi domin gaskiya ita ce ginshikin adalci.

Kalaman da aka jinginawa El-Rufa'i

Leadership ta wallafa cewa rikicin ya samo asali ne daga wani rubutu da ADC Vanguard ta wallafa a baya kafin ta goge shi.

A cikin sakon, an danganta wa El-Rufai cewa ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ce:

Kara karanta wannan

An bukaci a kashe Bello Turji kamar Shekau duk da ya nemi ya Mika Wuya

“Mafi cike da rashawa da rashin gaskiya a tarihin Najeriya.”

Rubutun ya kara da cewa dukkan bangarorin gwamnati, daga tattalin arziki zuwa tsaro sun gurguje saboda cin hanci da rashawa da kuma fifita ‘yan uwa da abokai.

El-Rufa'i da wasu 'yan siyasa a taron ADC a Abuja
El-Rufa'i da wasu 'yan siyasa a taron ADC a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

ADC Vanguard ta nemi afuwar El-Rufa'i

Bayan martanin tsohon gwamnan, kungiyar ADC Vanguard ta fito da sanarwa inda ta nemi afuwa tare da bayyana cewa ba ta da niyyar bata masa suna.

Ta ce:

“Muna neman afuwa kan wannan abin da ya faru. Ba mu yi shi da nufin bata maka suna ba, kuma za mu guji yin hakan a nan gaba.”

Kungiyar ta kuma bayyana cewa daga yanzu za ta rika amfani da sahihan shafuka da tushe na gaskiya kafin wallafa kowane sako.

Jamoh ya ce El-Rufa'i na APC

A wani rahoton, kun ji cewa wani jigon APC, Bashir Jamoh ya bayyana cewa har yanzu suna tare da Malam Nasir El-Rufa'i.

Legit Hausa ta rahoto cewa Jamoh ya bayyana haka ne yayin wani taro da manema labarai a jihar Kaduna.

A cewarsa, tsohon gwamnan ya bayar da gudumawa sosai waje kafa APC kuma har yanzu suna neman shawari a wajen hi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng