'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Plateau, an Kashe Mutane Tare da Bankawa Gidaje Wuta

'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Plateau, an Kashe Mutane Tare da Bankawa Gidaje Wuta

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi barna bayan sun kai harin ta'addanci a karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau
  • Miyagun sun hallaka mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba tare da bankawa gidaje wuta yayin harin da suka kai
  • Dakarun sojoji sun kai dauki bayan aukuwar lamarin inda suka fatattaki 'yan bindigan bayan an yi musayar wuta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Wasu 'yan bindiga da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kai mummunan hari a garin Tim, da ke cikin yankin Chakfem na karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau.

'Yan bindigan sun kashe mutane biyar tare da kone gidaje guda 10 a yayin harin da suka kai.

'Yan bindiga sun kai hari a Plateau
Hoton jami'an 'yan sanda a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Duk da yin sulhu, 'yan bindiga sun kashe manoma a Kaduna

'Yan bindiga sun kashe mutane a Plateau

Majiyoyi sun bayyana cewa harin ya auku ne a ranar Talata, 19 ga watan Agustan 2025, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma.

Maharan sun afka cikin garin inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi, sannan suka banka wa gidaje wuta.

Wasu majiyoyin cikin gari sun tabbatar da cewa an riga an kwashe gawarwakin waɗanda aka kashe domin yi musu jana’iza, yayin da waɗanda suka samu raunuka ke karɓar kulawa a asibitocin lafiya da ke kusa.

Mazauna yankin sun bayyana cewa lamarin na iya zama ramuwar gayya saboda zargin satar shanu da aka yi a yankin a baya-bayan nan.

Wannan ne ya sanya ake zargin cewa maharan sun dawo domin daukar fansa.

Dakarun sojoji sun kai dauki

Sojoji na rundunar Special Task Force (STF) sun isa wajen bayan samun rahoton harin, inda suka yi artabu da maharan.

Kara karanta wannan

Bayan kashe masallata, 'yan bindiga sun sake kona mutane a Katsina

Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun tilasta musu ja da baya, kuma ana kyautata zaton cewa wasu daga cikin maharan sun samu raunukan harbin bindiga a yayin musayar wutan.

Duk da cewa a ranar Laraba an samu ɗan sassauci a yankin, mazauna yankin sun ce al’ummar garin Tim har yanzu na cikin tsoro da fargaba saboda yiwuwar sake kai hari.

'Yan bindiga sun yi barna a Plateau
Taswirar jihar Plateau, Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Hukumomi sun tabbatar da cewa bincike yana gudana tare da kokarin gano waɗanda suka aikata wannan ta’addanci.

Mutane a yankin sun bayyana damuwarsu kan irin wannan hare-hare da suka yi ta addabar karamar hukumar Mangu a ’yan watannin da suka gabata.

Sun roki gwamnati da jami’an tsaro da su kara tsaurara matakai domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

'Yan bindiga sun kashe manoma a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun dirarwa manoman da ke kan hanyarsu ta komawa gida a jihar Kaduna.

'Yan bindigan sun hallaka manoma guda biyar bayan sun farmake su a wani kauye da ke cikin karamar hukumar Birnin Gwari.

Maharan dai sun kai harin ne duk da yarjejeniyar sulhu da gwamnatin Kaduna ta yi da su domin samun zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng