Sheikh Asada Ya Yi Watsi da Batun Sulhu da Bello Turji, Ya Kawo Mafita
- Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada, ya yi fatali da batun yin sulhu da jagoran 'yan bindiga, Bello Turji
- Sheikh Asada ya bayyana cewa ya kamata mutane su tashi su kare kansu maimakon tattauna da 'yan ta'adda marasa amana
- Hakazalika ya kuma karyata wani faifan murya da ake yadawa yana tattaunawa da Turji, inda ya ce tsoho ne ba na yanzu ba ne
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Sheikh Murtala Bello Asada ya yi tsattsauran suka kan kiran da Farfesa Abubakar Usman Ribah ya yi na a yi tattaunawa da fitaccen shugaban ’yan bindiga, Bello Turji.
Sheikh Asada ya bayyana kiran a matsayin abin da ba za a yarda da shi ba kuma barazana ce ga tsaron al’ummomi a Yammacin Arewa.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya sanya bidiyon da malamin yake magana a shafinsa na X.
Sheikh Asada ya soki sulhu da Bello Turji
Sheikh Asada ya yi wannan furuci ne a ranar Laraba yayin da yake mayar da martani ga maganganun Farfesa Usman Ribah na baya-bayan nan da ke goyon bayan tattaunawar gwamnati da ’yan bindiga a matsayin hanyar samar da zaman lafiya.
Ya yi kira ga mazauna kauyukan da ke fama da hare-haren ’yan bindiga da su ki amincewa da irin wannan kira, su rungumi kare kai maimakon dogaro da tattaunawa.
"Tattaunawa da Turji ba ita ce mafita ba. Jama’a bai kamata su ɓata lokaci da fata kan tattaunawa da wanda ya kashe, ya yi garkuwa, ya hallaka mutane ba."
"Abin da al’ummarmu ke buƙata shi ne su kare kansu, su kare iyalansu, su kuma tsaya tsayin daka kan waɗannan miyagun mutane.”
- Sheikh Murtala Bello Asada
Batun Asada ya tattauna da Turji
Shehin malamin ya kuma karyata wani sautin murya da ya bazu a shafukan sada zumunta, inda ake zargin shi ne aka ji yana tattaunawa da Turji.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa wannan sautin an ɗauke shi kusan shekaru biyar da suka gabata, don haka ba ya nuna matsayin da yake kai a halin yanzu game da shugaban ’yan bindigan.
"Akwai faifan sautin murya da ake yadawa, wannan karya ce, munafurcin masu munafurci ne. Ana yada shi ana cewa ga Murtala Bello Asada yana tattaunawa da Turji. Wannan karya ce."
"Kun san abin da ya faru, wasu munafukan Allah ne. Wannan wayar ta fi shekara biyar. Tun matakin farko ne, lokacin da muke ba da uzuri muna ganin 'yan ta'addan za su tuba."
- Sheikh Murtala Bello Asada
Yaran Bello Turji sun kashe soja
A wani labarin kuma, kun ji cewa yaran fitaccen jagoran 'yan bindiga, Bello Turji, sun kai haren-haren ta'addanci a Sokoto.
'Yan bindigan sun kashe mutane da dama ciki har da jami'in soja da wani dan sa-kai a hare-haren da suka kai.
Yaran na Bello Turji sun kuma yi awon gaba da mutane da dama zuwa cikin daji bayan sun gama cin karensu babu babbaka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

