Gyaran Ibada: Hukuncin Sallah da Tufafi Mai Dauke da Hoto a Musulunci
- Sheikh Jabir Sani Mai Hula ya bayyana cewa ba ya halatta yin sallah da riga mai dauke da hoto ko zane mai daukar hankali
- Ya ce yin hakan yana rage darajar ibada, duk da cewa sallar da aka yi tana inganta, amma an aikata abin da bai dace ba
- Malamin ya gargadi musulmi su guji sanya kaya masu dauke da hotuna ko zane a lokacin ibada domin samun nutsuwa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto – Sheikh Jabir Sani Mai Hula ya yi karin bayani kan hukuncin yin sallah da tufafi masu dauke da hoto ko zane, yana mai cewa hakan ba shi da inganci wajen ibada.
Tambayar ta taso ne bayan wani mutum ya nemi jin hukuncin sallar da aka yi da irin wannan kaya a wajen karatun da malamin ya gudanar.

Kara karanta wannan
Sheikh Pantami ya nuna bacin rai kan an bindige Musulmai 27 suna salla a masallaci

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da malamin ya yi ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Jabir ya ce musulmi na bukatar kula da tufafin da suke amfani da su wajen ibada domin kada su jawo hankalinsu ko rage darajar sallah.
Hukuncin yin sallah da tufafi mai hoto
Sheikh Jabir ya ce ba ya halatta yin sallah da riga mai dauke da hoto, ko na mutane, ’yan siyasa, ’yan wasan kwallo, malaman addini ko kuma wani mutum dabam.
Ya yi nuni da cewa ba wai kawai tufafin da ke dauke da hotuna ne ake gujewa ba, har ma da tufafi masu dauke da zane mai daukar hankali da zai iya kawo ruɗani a cikin ibada.
Malamin ya yi karin haske da hadisin da A’isha (RA) ta ruwaito cewa Annabi Muhammad (SAW) ya taba yin sallah da riga mai zane, amma ya ce ta shagaltar da shi, don haka ya umarci a cire ta.
Ya ce Nana A’isha (RA) ta rawaito, cewa:
“Manzon Allah (SAW) ya taba yin sallah da wani kaya mai zane, sai ya ce: ‘Wannan abu ya shagaltar da ni, ku kai shi wurin Abu Jahm ku kawo mini Anbijaniyyah (marar zane).’”

Source: Facebook
Ingancin sallah da tufafi mai hoto
Duk da gargadin da ya yi, Sheikh Jabir ya bayyana cewa sallar da aka yi da riga ko kaya mai hoto ta yi, amma mutum ya aikata abin da bai dace ba a shari’a.
A kan sake ibadar kuma, malamin ya ce ba a buƙatar maimaita sallah idan an riga an yi ta da irin wannan kaya.
Sallah ibada ce mai buƙatar nutsuwa da tawali’u, don haka bai kamata mutum ya sanya tufafi masu jan hankali ko dauke da hotuna ba.
Hukuncin kallon matar da za a aura
A wani rahoton, kun ji cewa malamin Musulunci, Dr Jamilu Zarewa ya yi magana kan kallon jikin matar da mutum zai aura.
Malamin ya ce malaman musulunci sun bayyana wuraren da ya kamata namiji ya kalla a jikin matar da ya ke so da aure.
Sai dai duk da haka, Sheikh Jamilu Zarewa ya ce akwai bukatar mutane su yi taka tsantsan wajen kallon domin kaucewa barna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

