Tinubu Ya Sanya Hannu kan Dokoki 40 a Shekaru 2, Ya Zarce Kokarin da Buhari Ya Yi
- Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan kudirori 40 a wata 24 na farkon mulkinsa, wanda ya zarce Shugaba Muhammadu Buhari
- Wani rahoto ya nuna cewa rattaba hannu kan dokokin 40 bai nuna tasirinsu ga al'umma ko ingancin shugabancin Tinubu ba
- Wannan na zuwa ne yayin da majalisar tarayya ta bayyana Tinubu a matsayin shugaban da ya fi kowa saurin sanya hannu kan dokoki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokoki a cikin shekaru biyu na farkon mulkinsa, fiye da na marigayi tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.
Rahoton Legis360 ya nuna cewa Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan dokoki 40 a shekaru biyu, wanda ya zarce 14 a Buhari ya sanya wa hannu.

Source: Twitter
Tinubu ya sanya hannu kan dokoki 40

Kara karanta wannan
"Ka ajiye Shettima": An gayawa Tinubu wanda ya fi dacewa ya zama mataimakinsa a 2027
Legis360, dandalin fasahar AI da ke inganta hulɗar majalisa a nahiyar Afirka, ce ta rubuta rahoton tare da haɗin gwiwar shirin PEI da kuma cibiyar PAACA, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya yi nazari kan tasirin kudurorin da shugaban kasar ya sanya wa hannu, da kuma alakar majalisar zartarwa ta kasa da majalisar tarayya ta 10.
A cewar rahoton, Tinubu ya amince da dokoki 40 tsakanin Yunin 2023 zuwa Mayun 2025 — wanda ya zarce dokoki 14 da Buhari ya rattaba hannu a farkon zangonsa tsakanin Mayun 2015 zuwa Mayu 2017.
Sai dai rahoton ya bayyana cewa ba lallai yawan dokokin da aka zartar su zamo masu tasiri ko nuna wani sakamakon shugabanci mai gamsarwa ba.
Rahoton Legis360 kan dokokin majalisa
A ranar Talata, shugaban Legis360, Samuel Folorunsho, ya bayyana cewa manufar dandalin shi ne ta cike gibi tsakanin gwamnati da wadanda ake mulka ta hanyar sauƙaƙa fahimtar dokoki, manufofi da tsare-tsare.
Folorunsho ya bayyana cewa ta amfani da sababbin hanyoyin fasaha, Legis360 na ƙoƙarin ba ‘yan Afirka, 'yan majalisa da ƙungiyoyi wata kafa ta inganta riƙon amana a mulki.

Kara karanta wannan
Kudin data, kira za su yi sauki, Tinubu ya dakatar da harajin 5% na kamfanonin sadarwa
"Mun fahimci cewa akwai wata dabi'a da ta samu gindin zama a cikin majalisa, inda za ka ga 'yan majalisar na murna kan kudurorin da suka amince da su, wadanda suka zarce wadanda aka sanya wa hannu.
"A binciken da muka yi, mun gano cewa dokokin da aka sanya wa hannu sun fi shafar al'umma fiye da wadanda majalisa ta amince da su, domin su ba su rika sun zama doka ba."
- Folorunsho.

Source: Twitter
An yaba wa kokarin Shugaba Tinubu
Sai dai wani rahoton jaridar The Guardian ya bayyana cewa dokoki 51 ne da majalisar dokokin ƙasa ta amince da su Shugaba Tinubu ya rattaba musu hannu a cikin shekaru biyu.
An ruwaito cewa shugaban kwamitin majalisa kan yada labarai da hulɗa da jama’a, Hon. Akin Rotimi, ya ce daga cikin jimillar dokoki 2,263 da aka amince da su, 51 ne shugaban ƙasa ya sanya wa hannu.
Hon. Akin Rotimi ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin “shugaban ƙasar da ya fi kowane rattaba hannu kan dokokin da aka gabatar masa a shekaru biyun farko na mulkinsa.”
Tinubu ya sanya hannu kan dokokin haraji
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan sababbin dokokin gyaran haraji huɗu, yana mai cewa "sabon babi ne ga Najeriya."

Kara karanta wannan
Minista ya kwararo yabo ga Tinubu, ya bayyana fannin da ya yi wa magabatansa zarra
Ana fatan waɗannan sababbin dokokin za su daidaita haraji, haɓaka kuɗin shiga, da inganta yanayin kasuwanci a Najeriya baki ɗaya.
An ji cewa dokokin sun haɗa da dokar haraji, dokar gudanar da haraji, dokar kafa hukumar haraji da kuma dokar kafa hukumar haɗin gwiwar haraji.
Asali: Legit.ng