Sheikh Pantami Ya Nuna Bacin Rai kan Bindige Musulmai 27 Suna Salla a Masallaci
- Ana cigaba da jimami kan kashe mutane 27 a lokacin sallar asuba a masallacin Mantau na Malumfashi, Katsina, inda wasu ’yan bindiga suka kai hari mai muni
- An bayyana cewa waɗannan mutane sun rasa rayukansu ne a cikin masallaci yayin da suke ibada, abin da ya nuna mugunta da rashin imani na masu kisan
- Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kamo waɗanda suka aikata laifin, tare da amfani da fasahohin zamani wajen bin sawun su
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ana cigaba da nuna bakin ciki bayan da wasu ’yan bindiga suka kai mummunan hari masallacin Unguwar Mantau da ke Malumfashi, Jihar Katsina.
An kashe mutane 27 a yayin sallar asuba, lamari ya girgiza zukatan musulmi da sauran al’umma baki ɗaya.

Source: Facebook
Tsohon Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, ya bayyana alhininsa a X tare da yin ta’aziyya ga iyalan mamatan da al’ummar Katsina baki ɗaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce mutanen sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke cikin ibada mafi girman lada da Annabi Muhammad (SAW) ya bayyana cewa ita ce mafi wuya ga munafukai.
Yadda aka kashe Musulmai a masallaci
Wakilan al’umma da jami’an asibiti sun tabbatar da cewa akalla mutane 27 ne suka rasa rayuka, yayin da wasu da dama suka samu raunuka a harin da aka kai masallacin.
Tsohon ministan ya ce hakan ta faru ne a lokacin da jama’a ke tsaka da sallar asuba, ibadar da take alamar imani da sadaukarwa.
Pantami ya ce Annabi Muhammad (SAW) ya bayyana cewa babu wata sallah da ta fi nauyi ga munafukai kamar sallar asuba da ta isha’i, amma kuma lada mai yawa ke tattare da su.
Malamin ya ce wannan ya nuna irin girman zaluncin waɗanda suka zabi kashe bayin Allah a lokacin ibada.
Sheikh Pantami ya nemi a dauki mataki
Pantami ya yi kira da a yi amfani da dukkan hanyoyin zamani wajen kamo masu laifin, musamman ta hanyar nazarin bayanan wayar hannu da tauraron dan adam.
Malamin ya ce wannan hanyar za ta taimaka wajen gano waɗanda suka kasance a yankin a lokacin da aka kai harin.
Ya kuma jaddada cewa kamata ya yi hukumomin tsaro su ɗauki wannan lamari da muhimmanci, domin irin wannan rashin imani na iya ci gaba da barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma.

Source: Twitter
Pantami ya yi ta’aziyya da addu’a
A ƙarshe, Pantami ya roƙi Allah ya karɓi waɗanda suka rasa rayuka a matsayin shahidai, ya ba iyalansu haƙuri da ƙarfin zuciya wajen jure wannan babban rashi.
Ya kuma yi addu’a Allah ya kunyata waɗanda suka aikata wannan babban laifi, tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.
'Yan bindiga sun yi hadari a Nasarawa
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da wani hadari da ya rusta da 'yan bindiga masu garkuwa.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama daya daga cikin 'yan bindigan da ya ce sun fito daga Abuja ne za su tafi jihar Filato.
Kakakin 'yan sandan jihar Nasarawa ya bayyana cewa an samu miliyoyin Naira a motar 'yan ta'addan da wasu makamai.
Asali: Legit.ng


