'Yan Daba Sun Yi Ta'asa, Sun Hallaka Jami'in 'Dan Sanda Har Lahira

'Yan Daba Sun Yi Ta'asa, Sun Hallaka Jami'in 'Dan Sanda Har Lahira

  • Wasu 'yan daba sun yi aika-aika a jihar Bayelsa bayan sun hallaka wani jami'in dan sanda har lahira
  • 'Yan daban wadanda ake zargin 'yan kungiyar asiri ne sun shammaci jami'in tsaron ne lokacin da yake dawowa daga wajen aiki
  • Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta bayyana cewa ana gudanar da bincke don cafke makasan da suka yi ta'asar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bayelsa - Wasu ‘yan daba da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne sun kashe wani ɗan sanda a jihar Bayelsa.

'Yan daban sun kashe dan sandan ne mai suna Oboh Goodluck a kusa da titin OMPADEC, a yankin Amarata na birnin Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

'Yan daba sun kashe dan sanda a Bayelsa
Shugaban rundunar 'yan sanda, Kayode Egbetokun, a wajen zantawa da manema labarai Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an harbe dan sandan ne wanda yake sanye da kayan gida, a safiyar ranar Talata yayin da yake dawowa daga aiki.

Kara karanta wannan

Kano: Yan sanda sun burma matsala bayan taimakon ɗan siyasa yana rabon kuɗi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan daba sun kashe dan sanda a Bayelsa

Ana zargin ’yan daban sun yi kokarin kwace wayarsa da wasu kayayyakin da yake ɗauke da su.

Al’ummar Amarata ta dade tana fuskantar rikicin kungiyoyin asiri tun watan Disamban bara, lokacin da wasu kungiyoyi biyu masu adawa da juna suka gwabza fada wajen nuna karfin iko.

Wannan yanayi ya haifar da tashin hankali a cikin al’ummar Amarata baki ɗaya, inda jami’an ’yan sanda suka mamaye yankin suna kama mutane, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Wasu mazauna yankin, sun bayyana cewa da safiyar ranar Talata, jami’an ’yan sanda dauke da makamai sun kai samame a wasu sassa na unguwar, suna harbi babu kakkautawa.

Rahotanni sun ce mafi yawan mazauna yankin sun tsere daga gidajensu domin guje wa fadawa hannun 'yan sanda.

Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya bayyana cewa jami’an ’yan sanda sun fasa tagoginsu yayin samamen, lamarin da ya bar al’ummar cikin fargabar barkewar sabon tashin hankali.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Ƴan sa kai sun yi wa ƴar bautar ƙasa tsirara, sun lakaɗa mata dukan tsiya

Sun roki jami’an tsaro da su yi taka-tsantsan, suna gargadin cewa idan aka bar lamarin ya tabarbare, zai iya haddasa karya doka da oda a babban birnin Yenagoa.

Unguwar Amarata, wadda ta kasance mai yawan jama’a a Yenagoa, na daga cikin wuraren da ake yawan samun rikici tsakanin kungiyoyin asiri da jami’an tsaro.

'Yan daba sun kashe dan sanda a Bayelsa
Hoton taswirar jihar Bayelsa, Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Bayelsa, DSP Musa Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin cafke waɗanda ake zargi da kisan.

'Yan sanda sun cafke jami'an hukumar INEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar 'yan sandan jihar Taraba sun kama wasu ma'aikatan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Hakazalika, 'yan sandan sun kwato kayayyakin zabe daga hannun jami'an na hukumar INEC bayan cafke su.

An dai cafke su ne bisa zarginsu karkatar da kayayyakin zabe na zaben cike gurbi na mazabar Karim Lamido I ta majalisar dokokin jihar Taraba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng