"Sun Mamaye Mazabata": Dan Majalisa Ya Fashe da Kuka kan Hare Haren 'Yan Bindiga

"Sun Mamaye Mazabata": Dan Majalisa Ya Fashe da Kuka kan Hare Haren 'Yan Bindiga

  • 'Yan bindiga sun addabi karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina da kai hare-haren ta'addanci ba kakkautawa
  • 'Dan majalisar da ke wakiltar Matazu a majalisar dokokin jihar Katsina, ya yi bayani cikin hawaye kan halin da suke ciki
  • Hon. Ibrahim Umar Dikko ya bayyana cewa mutanen mazabarsa sun kasa zuwa gonakinsu saboda tsaron harin 'yan bindiga

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Yan bindiga sun mamaye wasu gundumomi a karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina.

'Dan majalisar da ke wakiltar Matazu kuma babban mai tsawatarwa na majalisar dokokin jihar Katsina, Hon. Ibrahim Umar Dikko, ya fashe da kuka kan lamarin.

'Yan bindiga sun addabi mutane da kai hari a Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda a wajen wani taro Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ya fashe da kuka ne a gaban takwarorinsa yayin da yake bayani kan halin da mutanensa suke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan majalisa ya shiga damuwa kan harin 'yan bindiga

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari masallaci, mutane da dama sun mutu ana sallah

Ya bayyana yadda ’yan bindiga suka mamaye mafi yawan yankunan da ke cikin karamar hukumar Matazu wadda yake wakilta a majalisar.

'Dan majalisar ya bayyana cewa daga cikin gundumomi 10 da ke cikin Matazu, guda takwas sun koma hannun ’yan bindiga.

Ibrahim Umar Dikko ya ce zuwa gona ya gagari manoma saboda tsoron harin da 'yan bindiga suke kai musu.

Sannan ya bayyana cewa an kashe akalla manoma 12 a cikin gonakinsu a kwanaki biyu da suka gabata, rahoton Daily Post ya tabbatar.

“A jiya da safe, a wajen garin kusa da makarantar sakandare, sun kashe wani matashi sannan suka sace shanu hudu da ake amfani da su wajen ayyukan noma."
“A jiya sun kashe manoma biyar a gonarsu. A ranar da ta gabata kuma sun kashe manoma bakwai. Wallahi, ba za a iya zuwa gona ba. Muna cikin mawuyacin hali, muna bukatar taimako."

- Hon. Ibrahim Dikko Umar

'Yan bindiga sun addabi mutane a Katsina

Kalaman ɗan majalisar sun nuna irin yadda al’ummomi ke cikin damuwa a jihar Katsina, wadda ta shiga cikin jihohin da ke fama da rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya ba ɗalibai 308 tallafin karatu har N30m, an fadi yadda kowa ya samu

Har yanzu hare-haren ’yan bindiga suna ci gaba da addabar Katsina, wanda hakan ke sanya al’ummomi cikin tsoro tare da raba dubban jama’a da muhallansu.

'Yan bindiga na kai hare-hare a Katsina
Hoton taswirar jihar Katsina, Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A cikin watannin baya-bayan nan, kungiyoyin ’yan bindiga sun kai hare-hare a kauyuka, suna kai farmaki kan manoma, ’yan kasuwa, da mazauna karkara.

An kashe mutane da dama, an sace dabbobi, an lalata dukiyoyi, lamarin da ya tilasta wa mutane da yawa barin gidajensu domin tsira da rayuwarsu.

Wadannan hare-haren sun tarwatsa harkokin noma da sauran ayyukan tattalin arziki, abin da ya ƙara tsananta matsalar rashin wadataccen abinci da talauci a yankin.

Duk da ci gaba da ayyukan sojoji da karfafa tsaro, ’yan bindigan suna ci gaba da kai hare-hare, inda sau da dama suke fakewa a cikin dazuzzuka don kai sababbin farmaki.

'Yan bindiga sun kashe masallata a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari cikin wani masallaci a jihar Katsina.

'Yan bindiga sun kai harin ne a Unguwar Mantau cikin karamar hukumar Malumfashi lokacin da ake yin Sallar Asuba.

Miyagun dai sun kutsa cikin masallacin, sannan suka bude wuta kan mai uwa da wabi, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasuwar mutum 13.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng