Wata Sabuwa: An Hana Motocin Dangote Wucewa a Jihar Edo

Wata Sabuwa: An Hana Motocin Dangote Wucewa a Jihar Edo

  • Mai fafutukar kare hakkin Bil’adama, Martins Vincent Otse da aka fi sani da VDM, ya hana motocin Dangote wucewa a Edo
  • Ya ce sun dauki matakin ne domin kare jama’a daga hadura, inda suka ba mutanen cikin motar tallafi domin ci gaba da tafiya
  • VDM ya bukaci Aliko Dangote ya kula da direbobinsa saboda yawan hadura, yayin da kamfanin bai ce komai ba har yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo – Wani mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da VDM ya hana motocin kamfanin Dangote wucewa a kan titin Edo.

A cewar sa, matukin motar da suka tsare ba shi da lasisi, wanda hakan ke jefa rayukan al’umma cikin haɗari.

Lokacin da VDM ke tsare motocin Dangote a jihar Edo
Lokacin da VDM ke tsare motocin Dangote a jihar Edo. Hoto: Verydarkblackman
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce suna tsayar da motocin ne domin kare jama’a daga hatsarin da ya saba aukuwa a hanyar Edo zuwa Auchi.

Kara karanta wannan

Wuraren da suka halatta saurayi ya kalla a jikin macen da zai aura a Musulunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

VDM ya kuma bayyana cewa an bai wa mutanen motar da mafi yawansu daga Arewacin Najeriya suke tallafin kuɗi domin su ci gaba da tafiya ba tare da wahala ba.

Dalilin tsayar da motocin Dangote a Edo

VDM ya ce suna tsare motocin ne domin kare jama’a daga haɗura da direbobin kamfanin Dangote ke haddasawa.

Ya bayyana cewa an ba da umarni a bar motocin su ci gaba da tafiya da karfe 9:00 na dare bayan jama’a sun koma gidajensu.

Ya ce:

“Mun kula da lafiyar mutanen da ke cikin motar, sun samu kulawa, sannan mun tabbatar motar ta tsaya a bakin hanya.
"Mun dauki wannan mataki ne domin kare jama’a daga direbobin da ba su da lasisi.”

VDM ya ƙara da cewa Dangote ne attajirin da ya fi kowa arziki a Afirka, inda ya ke samun kaso mai yawa na kudinsa a Edo, amma direbobinsa na haddasa asarar rayuka a kan titunan jihar.

Kara karanta wannan

Alhaki ya kama su: 'Yan bindiga sun yi hadari bayan karbo makudan kudin fansa

Alhaji Aliko Dangote yana jawabi a wajen wani taro
Alhaji Aliko Dangote yana jawabi a wajen wani taro. Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

Kiran da VDM ya yi wa Dangote

Mai fafutukar kare jama'an ya yi kira ga shugaban kamfanin, Alhaji Aliko Dangote, da ya dauki matakan tabbatar da cewa direbobin sa suna bin ƙa’idojin tuki.

Ya ce:

"Mun bukaci Dangote ya binciki direbobinsa sosai kafin ya ba su mota.
Akwai wata yarinya ‘yar shekara 22 da direbansa mara lasisi ya murkushe, har ta shafe watanni 11 tana jinya a asibiti.
"Jiya ma wata motar sa ta hallaka mutum shida. Dole ya dauki matakin da ya dace.”

Ya bayyana cewa al’ummar Auchi ba su da wani zaɓi illa tsayar da motocin Dangote daga amfani da hanyoyinsu, har sai an kula da barnar da ake musu.

A halin yanzu, kamfanin Dangote bai yi wani martani kan lamarin ba, duk da cewa ana cigaba da hana motocinsa wucewa a yankin.

Dangote zai kafa sabon kamfanin siminti

A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya fara shirin kafa sabon kamfanin siminti a kasar Ivory Cost.

Kara karanta wannan

Gungun 'yan ta'adda sun kutsa masallaci a Sakkwato, sun budewa masallata wuta

Rahotanni sun bayyana cewa sabon kamfanin zai shiga jerangiyar masana'antun siminti sama da 10 da ya mallaka a ketare.

Masana tattalin arziki sun bayyana cewa hakan zai taimaka wajen kara habaka tattalin kasahsen Afrika da rage dokaro da kasashen waje.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng