"Sai an Yi Hakan": Shugaban ICPC Ya Samo Mafita ga Najeriya kan Matsalar Cin Hanci

"Sai an Yi Hakan": Shugaban ICPC Ya Samo Mafita ga Najeriya kan Matsalar Cin Hanci

  • Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, Musa Adamu Aliyu, ya tabo batun matsalar cin hanci da ta ki ci, ta ki cinyewa a Najeriya
  • Musa Adamu Aliyu ya bayyana cewa yin hukunci kadai, ba zai taba kawo karshen matsalar cin hanci a Najeriya ba
  • Shugaban na ICPC ya bayyana cewa dole ne sai an bi wasu hanyoyi kafin a samu damar shawo kan matsalar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, Musa Adamu Aliyu, ya yi magana kan matsalar cin hanci.

Shugaban na ICPC ya bayyana cewa amfani da hukunci kaɗai ba zai wadatar ba wajen yaki da cin hanci a Najeriya.

Shugaban ICPC ya yi magana kan cin hanci
Hoton shugaban hukumar ICPC, Musa Adamu Aliyu Hoto: @icpcnigeria
Source: Facebook

Musa Adamu Aliyu ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Maiduguri yayin jawabinsa na maraba a wani taron da aka gudanar a babban birnin na jihar Borno, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

ADC ta cimma matsaya da Atiku, Peter Obi da Amaechi kan batun takara a zaben 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron na rana daya na tattaunawa ne da dukkanin Antoni Janar na jihohin da ke yankin Arewa maso Gabas.

Shugaban ICPC ya koka kan cin hanci

Shugaban na ICPC ya ce dole ne Najeriya ta haɗa hanyoyi daban-daban domin kawo ƙarshen cin hanci.

A cewarsa, cin hanci ya kasance ɗaya daga cikin manyan matsalolin da suka daɗe suna addabar kasar nan, kuma ya taka rawa wajen raunana tattalin arziki, kara rashin tsaro da kuma sa jama’a kin yarda hukumomin gwamnati.

"Mun sani daga abin da muke gani a duniya, da kuma daga dokokinmu, cewa hukunci kaɗai ba zai isa ba."
"Dole ne mu haɗa hanyoyi da dama, mu dawo da kadarorin da aka sace, mu maido da adalci ga waɗanda aka zalunta, mu karfafa tsarinmu, kuma sama da komai, mu yi aiki tare tsakanin hukumomi da kuma yankuna."
"Ya ku mahalarta, cin hanci na ɗaya daga cikin mafi tsananin kalubale a wannan zamani. Yana raunana tattalin arziki, yana kara rashin tsaro, kuma yana rushe amincin jama’a ga gwamnati."

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa APC ta lashe mafi yawan zabukan cike gurbi da aka yi a Kano da jihohi 12'

"Duniya baki ɗaya tana magana da murya guda kan yaki da cin hanci, kuma Najeriya ba za ta bar kanta a baya ba."

- Musa Adamu Aliyu

Shugaban ICPC ya yabawa gwamnatin Borno

Musa Adamu Aliyu ya yaba wa gwamnatin jihar Borno bisa fifita gyaran tsarin shari’a, yana mai cewa irin wannan kokari zai taka muhimmiyar rawa a yaki da cin hanci, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Shugaban ICPC ya koka kan cin hanci a Najeriya
Hoton shugaban hukumar ICPC, Musa Adamu Aliyu, yana jawabi a wajen wani taro Hoto: @icpcnigeria
Source: Facebook
"A nan Arewa maso Gabas, mun sani sosai yadda cin hanci da raunanan hukumomi ke kara tsananta rashin tsaro da talauci."
"Amma kuma mun san karfin gyare-gyare. Bangaren shari'a na Borno, karkashin jagorancin babban alkalin jihar, ya kafa abin koyi ga kasa baki ɗaya wajen aiwatar da gyare-gyaren a fannin shari’a."

- Musa Adamu Aliyu

ICPC ta bankado badakalar N71.2bn

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaki da hanci da rahawa ta ICPC, ta bankado wata badakala a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Hukumar ICPC ta bayyana cewa akwai rashin gaskiya a shirin ba da lamuni ga dalibai n. NELFUND.

Ta bayyana cewa daga cikin N100bn da aka ware don shirin, N22.8bn kadai suka isa hannun dalibai da jami'o'i.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng