Gwamnan Taraba Ya Lakume N5.22bn kan zuwa Kasashen Waje? Gwamnati Ta Yi Bayani
- Wasu rahotanni sun fito masu nuna cewa gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya kashe biliyoyin Naira wajen yin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje
- Gwamnatin jihar Taraba ba ta gamsu da fitar wadannan rahotannin ba, inda ta bayyana cewa babu komai a cikinsu face karya
- Kwamishiniyar yada labaran jihar, Hajiya Zainab, ta bayyana cewa batun Gwamna Kefas ya kashe kudaden ba komai ba ne fa ce tatsuniyar gizo da koki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Taraba - Gwamnatin jihar Taraba ta yi martani kan rahoton da ke cewa Gwamna Agbu Kefas, ya kashe Naira biliyan 5.22 cikin watanni shida wajen tafiye-tafiye zuwa kasashen waje.
Gwamnatin jihar Taraba ta karyata rahoton tana mai cewa tsantsagwaron karya ce da kuma yaudara.

Asali: Twitter
Martanin gwamnatin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishiniyar yada labarai, Zainab Jalingo, ta fitar a ranar Lahadi, 18 ga watan Agustan 2025, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya yi nuni da bayanai daga shafin yanar gizon gwamnatin jihar da na hukumar kididdiga ta kasa (NBS), wadanda suka nuna gwamnan ya lakume makudan kudaden kan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje.
Gwamnatin Taraba ta yi watsi da rahoton yawo
Zainab Jalingo ta yi watsi da rahoton, tana mai cewa kage ne marar tushe, wanda babu hujjar tabbatar da shi, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
Kwamishiniyar ta bayyana cewa adadin da aka ambata ba ya cikin kasafin kuɗin jihar, ko shafin yanar gizon gwamnati, ko kuma bayanan da NBS ta fitar.
Ta shawarci jama’a su yi bincike da kansu kafin su yarda da irin wannan labari.
"Mun bincika, kuma muna bukatar jama’a su yi hakan. Kafin a yi hakan, zargin kashe Naira biliyan 5.22 ba komai ba ne face tatsuniya."
- Zainab Jalingo
An lissafo nasarorin Gwamna Agbu Kefas
Kwamishiniyar ta kuma jaddada nasarorin da gwamnatin ta samu musamman a ɓangaren ilimi, kiwon lafiya, da bunƙasa tattalin arziki, a matsayin hujjar ci gaba wanda yake a bayyane.
“Sauya al’amura hanya ce da ake bi a hankali wadda ke buƙatar tsari, yanke shawarar da ta dace, da kuma jajircewar aiki. Sakamakon hakan ya fara bayyana yanzu."
- Zainab Jalingo

Asali: Twitter
An bukaci jama'a su yi watsi da rahoton
Gwamnatin ta bukaci jama’a su yi watsi da rahoton kuma su dogara da hanyoyin hukuma wajen samun sahihin bayani.
Hakazalika, ta kuma sake tabbatar da jajircewarta kan gaskiya da kuma bin doka wajen gudanar da mulki.
Sheikh Kabir Gombe ya samu sarauta a Taraba
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanannen malamin addinin musulunci, Sheikh Kabir Haruna Gombe, ya samu mukamin sarauta a jihar Taraba.
Sheikh Kabir Gombe wanda shi ne sakataren kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'a Wa Igamatis Sunnah (Jibwis) na kasa, ya samu sarautar Modibbon Lau.
Hakimin Lau da ke karamar hukumar Lau a jihar Taraba, Alhaji Abdullahi Ibrahim na Chindo, shi ne wanda ya amince da nadin da aka yi wa Sheikh Kabir Gombe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng