An Yi Babban Rashi, Mahaifiyar Shugaban APC na Kasa Ta Rasu bayan Jinya

An Yi Babban Rashi, Mahaifiyar Shugaban APC na Kasa Ta Rasu bayan Jinya

  • Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya rasa mahaifiyarsa mai suna Mama Lydia Yilwatda 'yar shekara 83
  • An ce tsohuwar ta rasu ne a asibitin koyarwa na Jami’ar Jos a safiyar Lahadi bayan wata gajeriyar rashin lafiya da ta yi
  • APC a Plateau ta bayyana mutuwarta a matsayin babban rashi ga Yilwatda da iyalan sa, jam’iyyar da kuma cocin da ta ke zuwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau – Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya shiga cikin alhini bayan da ya rasa mahaifiyarsa, Mama Lydia Yilwatda, wacce ta rasu a safiyar Lahadi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Mama Lydia ta rasu tana da shekara 83 a duniya, a asibitin koyarwa na jami’ar Jos (JUTH), inda ta dade tana karɓar kulawa daga likitoci.

Kara karanta wannan

Fitaccen dan kasuwa a Arewa kuma na kusa da marigayi Shehu Shagari ya rasu

Shugaban APC, Farfesa Yilwatda da mahaifiyar shi.
Shugaban APC, Farfesa Yilwatda da mahaifiyar shi. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa kakakin APC a Plateau, Shittu Bamaiyi ne ya fitar da sanarwa yana bayyana mutuwarta a matsayin babban rashi da ya shafi iyalanta, jam’iyyar a kasa baki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahaifiyar shugaban APC na kasa ta rasu

Shittu Bamaiyi ya ce mutuwar Mama Lydia ta zo da firgici kasancewar ba wai kawai rashi ne ga Farfesa Yilwatda ba, har ma ga daukacin mambobin jam’iyyar APC a Plateau da ƙasar baki ɗaya.

Ya ce iyalan marigayiyar sun tabbatar da cewa ta rasu ne a safiyar Lahadi a JUTH bayan samun sauyin yanayi na rashin lafiya.

Bamaiyi ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai kishin addini, shugabar mata mai daraja, da kuma ginshiƙi a cocin Church of Christ in Nations (COCIN).

Gudumawar mamar shugaban APC

Sanarwar ta ce Mama Lydia tare da mijinta marigayi Toma Goshewe Yilwatda sun taka rawar gani wajen gina coci da wayar da kai a jihohi da dama ciki har da Borno, Yobe, Bauchi da Plateau.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon sakataren jam'iyyar PDP na kasa ya riga mu gidan gaskiya

A cewar jam’iyyar, irin rayuwa da gudummawar da ta bayar sun bar gagarumin tarihi da ba za a manta da shi ba, musamman wajen karfafa wa matan coci gwiwa da kuma tallafa musu.

Jam’iyyar ta ce wannan lamari ya nuna irin jajircewar marigayiyar wajen bautar Ubangiji da taimaka wa al’umma.

Shugaban APC, Farfesa Yilwatda a ofishinsa da ke Abuja
Shugaban APC, Farfesa Yilwatda a ofishinsa da ke Abuja. Hoto: All Progressive Congress
Source: Twitter

Tasirin mutuwar ga shugaban APC

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa kakakin jam'iyyar ya ce rashin ya zo a lokacin da ake bukatar mahaifiyar shugabansu sosai.

Bamaiyi ya ce:

“Mutuwarta babban rashi ne ga Farfesa Yilwatda, domin a wannan lokaci ne ake fi bukatar addu’o’i da shawarwarin uwa ga rayuwarsa da kuma jagorancinsa a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.”

Jam’iyyar APC a Plateau ta roƙi Allah ya bai wa iyalan marigayiya haƙuri da juriyar rashin, musamman lura da halin da shugabanta zai shiga.

Tsohon ministan Buhari ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ministan noma na kasa, Audu Ogbeh ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya da ya yi.

Rahotanni sun bayyana cewa Audu Ogbeh ya rike ministan noma ne a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari.

Bincike ya nuna cewa tsohon ministan ya rike mukamai daban daban a Najeriya, ciki har da minista a zamanin mulkin Shehu Shagari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng