Ansaru: Barnar da Jagogorin Yan Ta’adda Suka Yi da Ba Ku Sani ba Kafin Cafke Su

Ansaru: Barnar da Jagogorin Yan Ta’adda Suka Yi da Ba Ku Sani ba Kafin Cafke Su

  • Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya yi karin haske kan jagororin yan ta'adda da aka cafke
  • Ribadu ya bayyana cewa an kama manyan shugabannin kungiyar Ansaru da suka jagoranci harin gidan yarin Kuje
  • Daga cikin wadanda aka cafke akwai Mahmud Usman, wanda ake kira Abu Bara’a, da mataimakinsa Malam Mamuda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana yadda aka yi nasarar kama jagororin kungiyar Ansaru.

Ribadu ya ce jami’an tsaro sun samu nasarar cafke manyan shugabannin kungiyar ta’addanci ta Ansaru.

Ribadu ya bayyana barnar da Ansaru ta yi a Najeriya
Mallam Nuhu Ribadu yayin wani taro a birnin Abuja. Hoto: Nuhu Ribadu.
Source: Twitter

Yadda aka cafke shugabannin Ansaru a Najeriya

TheCable ta ce wadannan shugabanni ne ake zargi da jagorantar harin gidan yarin Kuje a shekarar 2022.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Samamen ya gudana ne tsakanin watan Mayu da Yuli na wannan shekara, inda aka sami bayanai daga leken asiri.

Kara karanta wannan

Saura Turji: Jami'an tsaro sun cafke shugaban kungiyar 'yan ta'addan Ansaru

Ribadu ya ce samamen an gudanar da shi tare da hadin gwiwar sojoji, hukumomin leken asiri da sauran jami’an tsaro.

Ya kara da cewa wadanda aka kama sun shafe shekaru suna cikin jerin gwanon da ake nema ruwa a jallo a Najeriya.

An gudanar da wannan aiki ne a cikin dajin Kainji da kewaye, inda kungiyar Ansaru ke da sansanoni da suka bazu har zuwa Jamhuriyar Benin.

Yadda jami'an tsaro suka cafke jagororin kungiyar Ansaru
Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa yayin wani taro a Abuja. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

Barnar da kungiyar Ansaru ta yi a Najeriya

Daga cikin wadanda aka kama akwai Mahmud Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a, shi ne ake cewa sarkin Ansaru kuma wanda ke shirya hare-haren garkuwa da mutane don tara kudi.

Haka kuma akwai mataimakinsa, Mahmud al-Nigeri, wanda aka fi kira Malam Mamuda, wanda ya taba yin horo a kasar Libya kan dabarun amfani da makamai da hada bama-bamai.

Ribadu ya bayyana cewa wadannan shugabanni suna da alaka da hare-hare da dama, ciki har da harin gidan yarin Kuje, kai hari kan ma’adanar uranium a Jamhuriyar Nijar, da kuma garkuwa da wasu shahararrun mutane a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana batun rashin lafiyar Tinubu, Gwamna Radda zai tafi jinya domin duba lafiyarsa

Ansaru: Nasarar da jami'an tsaro suka sama

Ya ce cafkarsu na nufin an rusa tsarin shugabanci na tsakiya na Ansaru, abin da ke nuna karshen wulakanci daga shugabannin ta’addanci.

Ribadu ya kara da cewa an kwato muhimman kayayyaki da shaidu na zamani daga hannun wadanda aka kama, cewar Vanguard.

Yanzu haka ana binciken su domin samun karin bayanai kan sauran mayakan Ansaru da hadin gwiwa da suke da shi da kasashen ketare.

Ya yaba wa shugaban kasa Bola Tinubu bisa jagora, da kuma jami’an tsaro bisa jarumtaka.

Gwamnatin Tinubu ta yiwa yan ta'adda ta yi

Kun ji cewa gwamnatin Bola Tinubu ta bayyana cewa lokaci ya yi da ƴan bindigar da suka addabi ƴan Arewa za su tuba su daina yin ta'addanci.

Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu ya gargarɗi ƴan ta'adda su miƙa makamansu domin samun zaman lafiya a Arewa.

Ribaɗu ya ce gwamnatin tarayya ta yi matukar kokarin a ɓangaren yaki da matsalar tsaro tun daga lokacin da ta karɓi mulki a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.