Goje: Farfesa Pantami Ya Kadu da Sanata Ya Yi Babban Rashi a Rayuwarsa

Goje: Farfesa Pantami Ya Kadu da Sanata Ya Yi Babban Rashi a Rayuwarsa

  • Tsohon ministan sadarwa, Isa Ali Pantami, ya mika sakon ta’aziyya ga Sanata Danjuma Goje bisa rasuwar ‘yarsa Hajiya Jummai
  • Pantami ya bayyana hakan a yau Lahadi, inda ya yi addu’ar Allah ya jikanta, ya ba iyalanta da duka ‘yan uwa haƙurin rashin
  • Ya ce za a yi jana’izar marigayiya a babban masallacin Abuja bayan sallar la’asar yau Lahadi, 17 ga Agusta, 2025

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Tsohon minsitan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami ya tura sakon ta'aziyya ga Sanata Muhammad Danjuma Goje.

Hakan ya biyo bayan rasuwar yar Sanata Goje a jiya Asabar 16 ga watan Agustan shekarar 2025 da muke ciki.

Yar Sanata Goje ta rasu a jiya Asabar
Tsohon gwamna, Danjuma Goje da yarsa, Jummai. Hoto: Muhammad Adamu Yayari.
Source: Facebook

Pantami ya yi ta'aziyya ga Sanata Danjuma Goje

Pantami ya sanar da haka ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a yau Lahadi 17 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

Fitaccen dan kasuwa a Arewa kuma na kusa da marigayi Shehu Shagari ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin rubutun, Pantami ya mika sakon ta'aziyyar ga tsohon gwamnan Gombe wanda ya mulki jihar daga 2003 zuwa 2011.

Ya yi ta'aziyyar ga dukan iyalan sanatan, yan uwa da abokan arziki kan wannan babban rashin da suka yi.

Tsohon ministan ya tabbatar da cewa za a yi sallar jana'izar marigayiyar a yau Lahadi bayan sallar la'asar a masallacin Abuja.

Pantami ya yi ta'aziyya da yar Goje ta rasu
Tsohon minista, Farfesa Isa Ali Pantami yayin wani taro a Abuja. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Addu'o'in da Farfesa Pantami ya yi ga marigayiyar

A karshe Isa Ali Pantami ya yi addu'ar Allah ya jikanta ya sa aljanna ce makomarta da sauran wadanda suka riga mu gidan gaskiya.

A cikin rubutunsa na ta'aziyya, Farfesa Pantami ya ce:

"Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji'un!
"Muna mika ta'aziyyar mu zuwa ga Mai girma Sanata Muhammad Danjuma Goje, bisa ga rasuwar 'ya gare shi, Hajiya Jummai.
Wanda za'a ma ta Sallar na babban masallacin Abuja a yau bayan Sallar Azahar in sha Allah.

Kara karanta wannan

Ana zargin sukar gwamnati ta jawo kai hari kan jigon APC, ya sha da ƙyar a Abuja

"Muna kara ta'aziyya zuwa ga dukkan iyalanta, da yan 'uwanta da abokan arziki, tare da adduar Allah ya sa Aljannah ce makomarta tare da iyayenmu da malamanmu da zurriyyarmu da yan'uwanmu."

Al'umma sun jajantawa Sanata Goje a Gombe

Al'ummar Najeriya da dama musamman daga jihar Gombe sun shiga jimami kan rasuwar Hajiya Jummai tare da yi mata addu'ar samun rahama.

Hakan ya biyo bayan soyayya da ake yi wa mahaifinta duba da irin ayyukan alheri da ya yi lokacin mulkinsa a jihar da kuma yanzu a mazabarsa.

Jigon PDP ya rasu a jihar Gombe

A baya, mun ba ku labarin cewa jam’iyyar PDP a Gombe ta yi babban rashi bayan rasuwar tsohon sakataren yankin Arewa maso Gabas, Kabiru Bappah Jauro.

Farfesa Isa Ali Pantami ya yi jimamin rasuwar Bappah Jauro inda ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin inda ya yi masa addu'ar samuj rahama a lahira.

Marigayin ya rasu a wani asibiti na Turkiyya da ke Abuja bayan fama da doguwar rashin lafiya, PDP ta ce rasuwar ta yi matuƙar taba ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.