Sulhu da Ƴan Bindiga Ya Yi Rana a Katsina, Manoma Sun Faɗi Alfanun Haka gare Su
- A wasu yankuna Katsina zaman lafiya ya fara dawowa bayan sulhun da al’umma suka yi da ’yan bindiga ba tare da gwamnati ba
- Manoma sun koma gonaki cikin kwanciyar hankali, inda wasu suka ce shekaru da dama basu yi noma ba amma yanzu rayuwa ta sauya
- Duk da wannan ci gaba, akwai yankuna da hare-hare ke ci gaba, inda aka yi garkuwa da mutane a Kankara, Sheme da Kakumi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - An samu sauki kan hare-haren yan bindaga a wasu kananan hukumomi a Katsina.
A cikin ƙananan hukumomin Jibiya, Batsari da Ɗanmusa a Katsina, al’umma sun yi sulhu da ’yan bindiga ba tare da gwamnati ba.

Source: Original
Wasu manoma sun koma gona a Katsina
Rahoton Aminiya ya ce wannan mataki ya taimaka wajen dawo da zaman lafiya a noman bana wanda ake yi a jihar Katsina..
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manoma sun fara komawa gonaki ba tare da tsoro ba inda suka tabbatar da cewa rabonsu da haka har sun manta a rayuwarsu.
Sai dai an tabbatar da cewa ba a ko’ina ba ake haka ba, wasu yankuna kamar Ƙanƙara da Faskari har yanzu na fama da hare-hare da garkuwa da mutane.
Manoma da dama a wuraren sun ce yawanci gonakin bakin gari ne ake noma, amma waɗanda ke nesa an bar su saboda tsoron hare-hare.
'Yan bindiga: Abin da manoma ke cewa bayan sulhu
Malam Salisu daga Jibiya ya ce har waɗanda ba su yi noman kankana ba a baya, yanzu sun yi kuma an fitar da ita zuwa Abuja da sauran kasuwanni.
A karamar hukumar Batsari da ke Katsina inda aka fara sulhun, yarjejeniyar na tafiya yadda ya kamata.
Hassan Dogon Faci ya ce:
“Garuruwan da suka kusan zama kufai yanzu duk noma ake yi, ranar Juma’ar da ta wuce har wa’azi muka je muka yi a garin Labo, ashe sai mu ce, an samu nasara.”

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Yan bindiga sun kutsa gidan Sarki da tsakar dare, sun sace ƴaƴansa

Source: Facebook
Mamakin da manoma ke yi kan sulhun
Surajo Jibiya ya ce abin ban mamaki shi ne, tsohon jagoran ’yan bindiga, Abdu Lanƙai, ya koma noma.
Alhaji Surajo Jibiya ya ce:
“Mun ga canji sosai, manomanmu duk sun koma gona, hatta cikin lunguna mun samu labarin sun ci gaba da noma, duk wata yarjejeniyar da aka yi da shi Lanƙai yana bin ta sau da ƙafa.”
Malam Rabe daga Nasarawa ya ce:
“Mu kam yanzu sai mu ce Alhamdulillahi. Lallai sulhu alheri ne a tsakanin al’umma.
“Jiya sai kusan magariba na baro gona, wanda can baya ƙarfe 12:00 ba ta yi mani. Rabinmu duk hijira muka yi.”
Katsina: An yi zaman sulhu da 'yan bindiga
Mun ba ku labarin cewa an samu fahimtar juna bayan sake zaman tattaunawar sulhu da yan bindiga a karamar hukumar Safana a jihar Katsina.
Karamar hukumar ta kulla yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindiga, kamar Jibia, Batsari, da Danmusa, domin samar da zaman lafiya.
Yarjejeniyar ta ba manoma damar noma cikin kwanciyar hankali, yayin da Fulani ke zuwa kasuwa da asibiti ba tare da tsangwama ba.
Asali: Legit.ng
