Bauchi: Hukumar BASIEC Ta Sanya Ranar Gudanar da Zaben Kananan Hukumomi

Bauchi: Hukumar BASIEC Ta Sanya Ranar Gudanar da Zaben Kananan Hukumomi

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Bauchi (BASIEC) ta shirya gudanar da zaben kananan hukumomi a fadin jihar
  • A cikin wata sanarwa da hukumar BASIEC ta fitar a ranar Asabar, ta bayyana cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomin ne a shekarar 2026
  • Hukumar BASIEC ta bayyana cewa sanar da lokacin gudanar da zaben, ya yi daidai da tanadin dokar zabe ta hukumar zabe ta kasa watau INEC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Bauchi (BASIEC) ta sanya lokacin gudanar da zaben kananan hukumomi.

Hukumar BASIEC ta sanar da ranar 17 ga watan Agusta, 2026, a matsayin ranar gudanar da zaɓen kananan hukumomi a fadin jihar.

Za a gudanar da zaben kananan hukumomi a Bauchi
Gwamna Bala Mohammed na Bauchi a wajen wani taro Hoto: @BalaMohammed
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce wannan sanarwar na ƙunshe ne a cikin wata takarda da aka fitar a ranar Asabar, 16 ga watan Agustan 2025 a Bauchi.

Kara karanta wannan

Zaɓen cike gurbi: Yadda 'yan sandan Kano su ka kama 'yan daba sama da 100

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Takardar sanarwar na dauke da sa hannun Ishiyaku Adamu, jami’in bayar da bayanai na hukumar BASIEC.

Hukumar BASIEC za ta gudanar da zaben Bauchi

Hukumar BASIEC ta bayyana cewa hakan ya yi daidai da tanade-tanaden dokar zaɓe ta 2022, wacce ta tsara cewa dole a yi irin wannan sanarwa akalla kwana 360 kafin ranar da aka tsara zaɓe, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Hukumar ta tuna cewa ko da yake sashe na 28 na dokar ya shafi zaɓuɓɓukan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ke gudanarwa kai tsaye, wannan tanadi ya shafi hukumar zaɓe ta jihohi (SEIC) ma.

"Kotun Koli a hukuncinta na ranar 20 ga Fabrairu, 2025, a kan jihar Rivers, ta yanke cewa wannan tanadi na doka ya zama sharadi tilas ga dukkan hukumomin zaɓe na jihohi."

- Ishiyaku Adamu

BASIEC ta kara da cewa Gwamna Bala Mohammed, a yunkurin nuna kishin bin doka da oda, ya amince tare da ba da umarni ga hukumar ta kiyaye tanadin dokar, ta hanyar bayyanawa a hukumance ranar zaɓen.

Kara karanta wannan

Zabe ya dauki zafi, ana zargin an sace yar takarar majalisar tarayya da wasu 25 a Kaduna

Hukumar ta bukaci jam’iyyun siyasa da jama’a baki ɗaya da su lura da wannan ci gaban yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaɓen kananan hukumomi a shekara ta 2026.

BASIEC za ta gudanar da zabe a Bauchi
Taswirar jihar Bauchi, Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta karin wasu labaran kan jihar Bauchi

Mukaddashin shugaban karamar hukuma ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Allah ya yi wani mukaddashin shugaban karamar hukuma a jihar Bauchi rasuwa.

Alhaji Wali Adamu wanda shi ne mukaddashin shugaban karamar hukumar Shirya ya koma ga mahaliccinsa.

Marigayin ya rasu ne a wani asibiti da ke a daidai lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Bauchi (BASIEC) ke shirin gudanar da zaben cike gurbi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng