Mummunan Hadari a Kano Ya Jawo Asarar Rayuka sama da 10
- Hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta Kano (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutane 12 a hadarin tirela a kauyen Samawa, Garun Malam a Kano
- Hadarin ya faru ne bayan wani sashe na wata ɗin tirela ya karye, ya kuma rabu da jikinta baki daya, lamarin da ya janyo motar ta shiga tangal tangal
- An tura gawarwakin mamatan zuwa asibitin Nassarawa, yayin da wadanda suka jikkata ke samun kulawa a asibitin da ke garin Kura
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen Kano ta tabbatar da afkuwar wani mummunan hadarin babbar mota da ya afku a kauyen Samawa, karamar hukumar Garun Malam, jihar.
Mai magana da yawun hukumar, Abdullahi Labaran, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai, daga ciki har da Legit Hausa.

Asali: Original
Jaridar Punch ta wallafa cewa Kakakin hukumar ya ce binciken farko ya nuna cewa hadarin ya faru ne sakamakon matsala da motar ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda hadari ya faru a Kano
Kakakin FRSC, Abdullahi Labaran hadarin ya shaida wa majiyar Legit cewa lamarin ya faru ne a safiyar Juma’a, 15 ga watan Agusta, 2025.
Haɗarin da ya afku, a kauyen Samawa da ke kan titin Zariya zuwa Kano, ya jawo asarar rayuka da dama.
Ya ce matsala da motar ta samu ya jawo wani bangare na burkinta ya fice, lamarin da ya jawo aka mummunan hadarin da ya salwantar da rayukan jama'a 12.
Abdullahi Labaran ya bayyana cewa:
“An samu rahoton hadarin da2:40 na safe. Motar da ta yi hadarin ita ce DAF Trailer CF95, mai lambar rajista KMC 931 ZE, wacce ke dauke da kaya ciki har da kayan yaji na Ajinomoto tare da fasinjoji.”
Ya ce jimillar mutane 19 ne ke cikin motar a lokacin hadarin, inda mutane 12 suka mutu, biyar suka ji rauni, yayin da biyu suka tsira ba tare da rauni ba.
An kai gawarwaki zuwa asibitin Kano
Kakakin ya kara da cewa an ajiye gawarwakin mamatan a asibitin Nassarawa, yayin da wadanda suka jikkata aka garzaya da su zuwa asibitin Kura domin samun kulawar gaggawa.
Kwamandan hukumar na Kano, CC MB Bature, ya ziyarci wurin hadarin, inda ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka mutu tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

Asali: Facebook
Bature ya jaddada bukatar direbobi su rika bin ka’idojin hanya da zirga-zirga don kauce wa irin wannan mummunan hadari.
Ya ce wadanda aka samu da karya doka za su fuskanci hukunci mai tsanani domin a dakile afkuwar hakan a gaba.
'Yan sandan Kano sun shirya zabe
A wani labarin, mun wallafa cewa Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta sanar da cewa jami’an tsaron jihar, ciki har da kungiyoyin bijilanti da jami’an KAROTA, ba za su shiga rumfunan zabe ba.
Rundunar ta bayyana haka ne a lokacin da ake shirin zabukan cike-gurbi da za a gudanar ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025, a kananan hukumomi da ke sassan jihar.
Kakakin hukumar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an kafa dokar hana zirga-zirga daga 12:00 na dare ranar Juma’a, 15 ga watan Agusta, har zuwa 6:00 na yamma ranar Asabar
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng