Dalilin da Ya Sa Malaman Addini Suke Sukar Asadus Sunnah kan Haduwa da Turji
Jihar Zamfara - Malamin addinin musulunci, Sheikh Musa Yusuf Asadus-Sunnah, ya shiga cikin daji domin tattaunawa da hatsabibin dan bindiga, Bello Turji.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Sheikh Yusuf Musa Asadus Sunnah dai ya jagoranci wasu malaman musulunci ne zuwa dajin Fakai da ke karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara, don tattaunawar sulhu da Bello Turji.

Source: Facebook
Musa Asadus Sunnah ya tattauna da Bello Turji
Malamin addinin musuluncin dai ya bayyana hakan ne a wani bayani da ya yi cikin wani faifan bidiyo da ya sanya a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi bayanin cewa mutanen Shinkafi ne suka neme su da bukatar su tunkari hatsabibin dan bindigan domin a yi sulhu.
Hakazalika ya bayyana cewa ganawarsu da Bello Turji ta sanya ya sako wasu mutane da ke rike a hannunsa wadanda aka yi garkuwa da su.
Sai dai, wannan batun sulhun ya jawo martani daga malaman addini wadanda ke kallon cewa akwai wata makarkashiya a ciki.
Malaman sun yi raddi ga Sheikh Asadus Sunnah kan batun sulhun da yake cewa ana kokarin yi da Bello Turji.
Malamai sun soki Sheikh Asadus Sunnah
Malamin addinin musulunci, Sheikh Murtala Asada na daga cikin masu sukar Asadus Sunnah kan batun tattaunawa da Bello Turji.
A cikin wani bidiyo da wani mai amfani da @AM_Saleeem a shafin X ya sanya, Sheikh Murtala Asada, ya yi martani mai zafi ga Asadus Sunnah.
Malamin ya bayyana cewa batun sulhu da Bello Turji ba komai ba ne fa ce karya domin bai ajiye makamansa ba.

Source: Facebook
Murtala Asada ya yi zargin cewa gwamnati ce ta dauki nauyin su Asadus Sunnah domin tattaunawa da su Bello Turji.
1. Karyar Turji ya ajiye makamai
Sheikh Murtala Asada ya bayyana cewa 'yan siyasa sun sanya Asadus Sunnah ya yi karyar cewa Bello Turji ya ajiye makamai.
Ya bayyana cewa ko kadan Turji bai ajiye makamai ba, kuma idan akwai wanda ya musanta hakan, ya zo su tattauna a kan matsalar.

Kara karanta wannan
Ana jita jitar rashin lafiyar Tinubu, Sanata ya fadi halin da Shugaban kasa ke ciki
Malamin ya kuma musanta cewa Turji ya ba da makaman da yake ta'addanci da su.
Ya bayyana cewa makaman da Bello Turji ya ba da na wasu jami'an tsaro ne da ya kashe lokacin da aka yi kokarin kai masa hari.
2. Ikirarin Turji ya daina ta'addanci
Malamin ya bayyana cewa ikirarin da Asadus Sunnah ya yi kan cewa tun daga ranar da suka je wajensa, Bello Turji, bai sake kashe kowa ba, karya ce tsagwaronta.
Ya kawo misalan hare-haren ta'addancin da Bello Turji ya kai bayan tattaunawar da suka yi da su Sheikh Asadus Sunnah.
3. Karbar kudi daga gwamnati
Sheikh Murtala Asada ya yi zargin cewa 'yan kwamitin Asadus Sunnah suna karbar kudi don yin abin da gwamnati take so.
Ya bayyana cewa N200,000 ake ba su shiyasa suke fitowa suna kare gwamnati. Sai dai Legit Hausa ba ta da tabbacin wannan zargi.
4. Musulunci ya yarda a yaki 'yan ta'adda
Sheikh Ishaq Adam na daga cikin malaman da ke da fahimtar tattaunawa da 'yan ta'adda ba ta da amfani ko kadan.
A cikin bidiyo da aka sanya a shafin Karatuttuka. Malaman Musulunci a shafin Facebook, malamin ya yi martani kan batun tattaunawa da 'yan ta'adda.
Malamin ya ce ko kadan bai tare da masu fahimtar wai a yi sulhu da 'yan ta'addan da ke cikin daji suna kashe mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Sheikh Ishaq Adam ya bayyana abin da Musulunci ya ce game da su da kuma hukuncin da ya kamaci a yi musu bayan haka.
"Kuma wadannan mutanen da ake ta cewa a yi sulhu da su ina da tambaya, menene matsayin Musulunci a kan irinsu?
"Musulunci abin da ya ce shi ne a yake su, a kashe su har sai sun daina wannan barnar."
"Musulunci ya ce ko a kashe su, ko a tsire su ko a yanke kafar dama da hagu ko a kore su daga garin."
- Sheikh Ishaq Adam
Yaran Bello Turji sun kai hari
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan ta'adda da ake zargin yaran Bello Turji ne sun kai hari a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan
Ta fara tsami: Shehi ya gorantawa Murtala Asada game da tattaunawa da Bello Turji
Miyagun 'yan ta'addan sun hallaka mutum daya tare da yin awon gaba da wasu mutum 16 yayin harin da suka kai.
Majiyoyi sun bayyana cewa wani na hannun daman Bello Turji mai suna Kallamu ne ya jagoranci 'yan ta'addan wajen kai harin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
