Ran Sarki Ya Ɓaci: Masarautar Kano Ta Tuɓe Rawanin Mai Unguwa, Ta Jero Laifuffukansa
- Masarautar Kano ta sauke Mai unguwa saboda zargin karya doka, kin amsa umarnin Sarki da cin amanar al’umma
- Sarkin Kano ya gargadi sauran masu rike da sarauta da su guji rashin gaskiya da neman abin hannun talakawa, domin kare martabar masarauta
- Masarautar ta ce ba za ta lamunci duk wani basarake a Kano da ke sabawa ka’ida da amanar da aka dora masa ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Masarautar Kano ta ɗauki mataki mai tsauri kan wani mai rike da sarautar gargajiya a jihar saboda saɓa doka.
Sarkin Kano ya sauke wani mai unguwa kan wasu laifuffuka da suka saba ka'ida da kuma cin amanar al'umma wanda Masarautar ta ce ba za ta lamunta ba.

Asali: Twitter
Hakan na cikin wani faifan bidiyon YouTube da Sarauta TV ta wallafa a daren yau Alhamis 14 ga watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan
Abba Gida Gida ya yi wa matasa albishir, ya faɗi tanadin da gwamnatinsa ta yi masu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zargin Mai Unguwa da saba ka'idoji a Kano
Daga cikin laifuffukan da ake zargin basaraken sun hada da saba da tsarin Masarautar da kuma rashin mutunta Sarki wanda babban laifi ne da ba a lamunta a ko ina.
Hakan ya janyo aka kwabe rawanin Mai Unguwar Yan Doya tare da gargadin sauran masu makamai da su kiyaye saba dokoki da kuma rashin bin umarni.
Masarautar ta ce ta samu Malam Murtala Husaini da laifuffukan da suka hada da kin amsa umarnin Sarki a lokuta da dama.
Sauran sun hada rashin zamansa a cikin talakawansa wanda hakan ya sabawa ka’idar amanar da aka ba shi.

Asali: UGC
Gargadin Sarki Sanusi II ga masu Unguwanni
Don haka Mai martaba Sarkin ta bakin babban dan majalisarsa, Matawallen Kano ya ba da umarnin sauke Mai unguwar daga kan mukaminsa.
Masarautar Kano ta ce ba za ta lamunci duk wani rashin gaskiya da cin amana daga kowanne mai rike da sarautar gargajiya ba.
Har ila yau, ya yi kira da sauran masu rike da sarauta da su guji rashin gaskiya da neman abin hannun talakawansu.
Matsalolin da Masu Unguwanni suke fadawa
Masarautar ta ce aikata irin wannan ya saba ka'idoji da kuma al'adun jihar da na Hausawa baki daya.
Masu unguwanni dai na daga cikin masu sarauta da ake yawan samun matsala da su musamman alaka tsakaninsu da talakawansu a kusan ko ina.
Ana yawan samunsu da almundahana musamman a bangaren sayar da filaye da sauran lamura da suka shafi talakawansu kai tsaye.
Ali Jita ya samu sarautar gargajiya a Kano
A baya, mun ba ku labarin cewa fitaccen mawaki Ali Jita ya samu sarautar mai unguwa a 'Ado Bayero Royal City' a Darmanawa, Kano a bikin nadin da aka gudanar.
Hakimin Darmanawa, Sarkin Yakin Kano, ya ja hankalin sababbin masu sarauta da su rike gaskiya da amana wajen sauke nauyin al’umma.
Tun farko, Ali Jita ya gayyaci jama’a a ranar Juma’a domin taya shi murna da addu’o’i, bikin ya gudana a ranar Asabar da safe a fadar Hakimin Unguwa Uku.
Asali: Legit.ng