Amurka Na Shirin Sayar wa Najeriya Bama Bamai Masu Linzami da Wasu Makamai

Amurka Na Shirin Sayar wa Najeriya Bama Bamai Masu Linzami da Wasu Makamai

  • Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta amince da sayar wa Najeriya kayan yaki da suka hada da bama-bamai da sauransu
  • Hukumar DSCA ta ce wannan zai taimaka wajen kara karfin Najeriya wajen yaki da ‘yan ta’adda da kuma hana safarar makamai
  • Manyan kamfanonin da za su samar da kayan sun hada da Lockheed Martin, RTX Missiles and Defence da BAE Systems

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. United States of America– Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta amince da yiwuwar sayar wa Najeriya kayan yaki.

Daga cikin makaman da za a sayar mata akwai bama-bamai masu linzami da roka, wadanda kudinsu ya kai dala miliyan 346, kimanin Naira biliyan 530.

Donald Trump da Bola Tinubu
Amurka za ta sayar wa Najeriya makamai Hoto: Donald Trump/Bayo Onanuga
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa wannan na kunshe ana wata sanarwa da Hukumar Defence Security Cooperation Agency (DSCA) ta fitar a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

PDP ta sacewa magoya bayan Jonathan da Obi guiwa da aka kafa kwamitin karba karba

Najeriya za ta sayi kayan yaƙi daga Amurka

The Guardian ta wallafa cewa hukumar DACA ta bayyana cewa Najeriya ta nemi sayen bama-bamai 1,002 MK-82 masu nauyin fam 500 kowanne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai kuma kayan hada makaman 1,002 MXU-650 Air Foil Groups (AFGs), da ƙarin wasu manyan makaman kai hari 5,000 da injin roka MK66-4, tare da wasu kayan aiki na musamman.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
Ana sa ran bama-baman za su taimakawa Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Har ila yau, kunshin kayan ya hada da wasu sassan bama-bamai, harsasai na gwaji da na yaki, da kuma fasahar sufuri daga gwamnatin Amurka da wasu kamfanoni.

Kamfanonin da za su sayarwa Najeriya makamai

DSCA ta bayyana kamfanonin da za su samar da kayan a matsayin Lockheed Martin, RTX Missiles and Defence, da kuma BAE Systems.

Lockheed Martin sananne ne wajen kera jiragen yaki, makamai masu linzami, da tsarin kare sararin samaniya, ciki har da jiragen yaƙi da roka.

RTX kuwa shi ne kamfani na biyu mafi girma a harkar kera makamai a duniya, yana samar da injinan jirage, makamai masu linzami, na’urorin gano abokan gaba, da tsare-tsaren tsaron kwamfuta.

Kara karanta wannan

Gungun 'yan ta'adda sun kutsa masallaci a Sakkwato, sun budewa masallata wuta

BAE Systems, da hedikwatarta ke Landan, ita ce babbar mai kera kayan yaki a Turai, tana samar da jiragen yaki, makamai, jiragen ruwa na yaki, manyan motocin sulke, da kayan lantarki na tsaro.

A cewar DSCA:

“Wannan yarjejeniyar za ta tallafawa manufofin harkokin wajen Amurka da tsaron kasa, ta hanyar kara tsaron abokin hulda na dabarun yaki a yankin Afrika ta Kudu da Sahara.”

Ta kara da cewa:

"Hakan zai inganta damar Najeriya wajen ti'unkarar barazanar da ake fuskanta yanzu da nan gaba, ta hanyar yaki da kungiyoyin ta’addanci da kuma hana safarar haramtattun kayayyaki a Najeriya da Tekun Guinea."

Amurka da wasu ƙasashe za su shigo Najeriya

A baya, mun wallafa cewa Gwamnatin tarayya tana tattaunawa da Saudiyya, Birtaniya, Amurka, Australia da wasu ƙasashe don samar da ayyukan yi ga ’yan Najeriya

Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyukan Yi, Muhammad Maigari Dingyadi, ne ya sanar da haka a Abuja ranar Talata, a ƙoƙarin gwamnati na samar da abin yi.

A cewar ministan, wannan shiri na daga cikin dabarun gwamnati na magance matsalar rashin aikin yi da zaman kashe wando musamman a tsakanin matasa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng