Ana cikin Yaɗa Jita Jitar ba Shi da Lafiya, Tinubu Zai Bar Najeriya Gobe Alhamis
- Shugaba Bola Tinubu zai tashi daga Abuja ranar Alhamis 14 ga watan Agustan 2025 domin halartar wasu taruka a ƙasashe duniya
- Haminsa a ɓangaren yada labarai ya tabbatar da cewa shugaban zai tafi Japan da Brazil, inda zai halarci taro da ganawa da shugabanni
- A Japan, zai halarci taron TICAD9 mai taken "Co-create Innovative Solutions with Africa" domin inganta tattalin arziki da jari-hujja
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Ana tsaka da yada rade-radi cewa ba shi da lafiya, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai bar Najeriya.
Bola Tinubu zai bar Abuja ranar Alhamis, 14 ga Agustan 2025 zuwa kasashen Japan da Brazil bayan ya tsaya a Dubai.

Asali: Twitter
Bola Tinubu zai bar Najeriya ranar Alhamis

Kara karanta wannan
Magana ta kare, bidiyon Shugaba Tinubu ya bayyana ana tsaka da jita jitar ba shi da lafiya
Hadiminsa na musamman a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga shi ya tabbatar da haka a shafin X a yammacin yau Laraba 13 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce Tinubu zai kuma tsaya a birnin Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa kafin ci gaba da tafiya zuwa Japan.
A Japan, Tinubu zai halarci Taron Tokyo karo na tara kan cigaban Afrika (TICAD9) a birnin Yokohama daga 20 zuwa 22 ga watan Agustan 2025.
Taken taron na bana shi ne "Co-create Innovative Solutions with Africa", wanda zai mayar da hankali kan bunkasa tattalin arzikin Afrika ta hanyar jari-hujja da kirkire-kirkire.
Tarukan da Tinubu zai halarta a kasashen duniya
Haka kuma, zai halarci zaman taruka, ya gana da shugabanni, da kuma kamfanonin Japan masu zuba hannun jari a Najeriya don kara hadin kai.
An fara taron TICAD ne a shekarar 1993 da gwamnatin Japan tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya, UNDP, kungiyar Afrika, da Bankin Duniya.

Kara karanta wannan
'Za mu more': An faɗi dalilai da ke nuna Jonathan ne mafi dacewa da bukatun Arewa
Taron na gudana duk bayan shekaru uku a Japan ko cikin kasashen Afrika, inda na baya ya kasance a Tunisia a watan Agustan 2022.

Asali: Facebook
Shugaban Brazil ya tura gayyata ga Tinubu
Bayan kammala taron TICAD9, Tinubu zai tafi birnin Brasilia a Brazil, don ziyarar aiki daga ranar Lahadi 24 zuwa Litinin 25 ga watan Agustan 2025.
Ziyarar ta biyo bayan gayyatar shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, inda za su yi ganawar bangarori biyu da tattaunawa kan harkokin kasuwanci.
Shugaban Najeriya zai kuma halarci taron kasuwanci da ‘yan kasuwar Brazil da kuma rattaba yarjejeniyoyi da fahimtar juna tsakanin kasashen biyu.
Za a samu ministoci da manyan jami’an gwamnati cikin tawagar shugaban, kamar yadda Bayo Onanuga ya bayyana.
Tinubu ya jagoranci taron majalisar zartarwa
Kun ji cewa hadimin shugaban kasa, Abdul'aziz Abdul'aziz ya fitar da faifan bidiyon da ke nuna Bola Tinubu a dakin taron Majalisar Zartarwa (FEC).
Hakan ya biyo bayan jita-jitar da ke ci gaba da yawo kan lafiyar shugaban kasa wanda ta zo karshe da bidiyon Shugaba Tinubu ya bayyana a yau Laraba 12 ga watan Agustan 2025.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume na cikin wadanda suka halarci taron a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Asali: Legit.ng