Matasa Sama da 100,000 Za Su Amfana a Sabon Shirin da Aka Kaddamar a Bauchi
- Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya kaddamar da wani sabon shirin ba da horo a fannoni daban-daban na fasahar zamani
- Shirin, wanda gwamnatin Bauchi ta yi hadin gwiwa da hukumar NITDA zai amfanar da matasa akalla 100,000 ta hanyar ba su horo daga nan zuwa 2027
- Gwamna Bala ya bayyana cewa shirin zai ba matasa damar gogewa a harkar fasahar zamani, wanda za su samu ayyukan yi a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi - A yunƙurin ganin Bauchi ta zama cibiyar kirkire-kirkire da fasaha na zamani, Gwamna Bala Mohammed, ya kaddamar da shirin Cybernations, wani tsari na horaswa kan tsaron yanar gizo.
Wannan shiri, wanda aka fi sani da aka fi sani da Digital Literacy and Skill Framework Bauchi Initiative, an ƙirƙire shi ne tare da haɗin gwiwar Hukumar Ci gaban Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA).

Source: Twitter
Gwamna Bala ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X tare da hotunan kaddamar da shirin a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shirin zai ba matasa akalla 100,000 horo
Ana sa ran wannan sabon shiri zai ba da horo na ƙwarewar zamani a fannoni daban-daban ga matasa sama 100,000 kafin shekarar 2027.
Da yake jawabi a wajen kaddamarwar a Bauchi, Gwamna Bala Mohammed ya ce wannan shiri “na nuna sabon babi a makomar tattalin arzikin jiharmu."
A cewarsa, shirin zai tabbatar da cewa ’yan ƙasa, musamman matasa, sun samu gogewa da damar shiga harkokin tattalin arzikin zamani na duniya.
Ya ƙara da cewa, shirin mai suna DL4ALL a takaice zai samar da ilimin zamani a makarantu da ma’aikatu, tare da samar da hazikan ma’aikata ga masu ɗaukar aiki na cikin gida da ƙetare.
Yadda matasan Bauchi za su amfana da shirin
Ya kuma bayyana cewa za a ba matasa 2,000 horo na musamman a fannonin fasaha da aka fi buƙata irin su ƙirƙirar manhaja, fasahar AI, tsaron yanar gizo, da sauransu.
“Mun gane cewa fasahar sadarwa a yau da nan gaba ita ce ke habaka cikin sauri, kuma tana da ƙarfin ɗaukar matasa masu ƙwarewa.
"Amfaninta shi ne mutum zai iya samun horo, ya samu takardar shaidar ƙwarewa, sannan ya dogara da ita wajen samun halal.
“Manufarmu a bayyane take, muna son sauya Bauchi zuwa jihar zamani, mai bunƙasar tattalin arziki, kuma mai ƙarfafa kirkire-kirkire.
Muna son amfani da fasaha ba a wajen aiki kadai ba, har da zama silar bunkasa tattalin arziki, ci gaban ɗan adam, da sauyin zamantakewa.”
- Gwamna Bala Muhammed.

Source: Twitter
A nasa bangaren, Manajan Darakta na kamfanin Galaxy Backbone, Farfesa Ibrahim Adeyanju, ya jaddada muhimmancin sanin dabarun tsaron yanar gizo a wannan zamani na fasaha.
Ya bayyana buƙatar haɗin kai don bai wa ’yan Najeriya ilimi da kayan aiki da za su ba su damar yin fice a duniyar zamani.
Daukar aiki: Kasashe za su hada kai da Najeriya

Kara karanta wannan
Ana batun yunwa, gwamnatin Tinubu ta fitar da ton 42,000 na hatsi a raba wa jihohi
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya za ta hada kai da wasu kasashen duniya domin samar sa ayyukan yi ga 'yan Najeriya.
Wannan shiri na daga cikin tsare-tsaren gwamnati na magance matsalar rashin aikin yi da zaman kashe wando tsakanin matasa.
Kasashen da gwamnatin ta ce ta fara tattaunawa da su don samar da ayyuka ga matasa sun hada da Saudiyya, Amurka da sauransu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

