Ana Jita Jitar Rashin Lafiya, Tinubu Ya Yi Magana, Ya Fadi Gwamnonin da Zai Yi Alaƙa da Su
- Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da hadin gwiwa da duk jihohin da suka jajirce wajen ci gaban dan Adam da tattalin arziki
- Ya bayyana haka ne bayan ganawar sirri da Gwamna Chukwuma Soludo, inda suka tattauna kan sauye-sauyen gwamnati
- Soludo ya ce ganawar ta kasance mai dadi, yana kuma tabbatar da tsohuwar zumuncinsu mai tsawon shekaru 20
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya gana da gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Chukwuma Soludo a Abuja.
Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da jihohin da ke jajircewa wajen ci gaban dan Adam, zamantakewa da tattalin arziki.

Asali: Twitter
Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Laraba 13 ga watan Agustan 2025 ta cikin wata wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan
Zai koma APC ne? An ga gwamnan adawa ya sanya hula mai tambarin Tinubu a Aso Rock
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rashin lafiya: Fadar shugaban kasa ta kare Tinubu
Tinubu ya bayyana haka ana tsaka da jita-jitar cewa yana fama da matsanancin rashin lafiya wanda ya jawo maganganu.
Hakan ya zo a daidai lokacin da aka ce ya kwashe kwanaki bai fito aka ganshi a bainar jama'a ba wanda ya saka shakku a zukatan yan Najeriya.
Sai dai fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwa inda take musanta abin da ake zargi da cewa Tinubu yana cikin koshin lafiya.

Asali: Facebook
Shugaba Tinubu ya yabawa Gwamna Soludo
Hakan na zuwa ne bayan ya karbi bakuncin Gwamna Chukwuma Soludo a fadar shugaban kasa.
Tinubu ya yabawa Gwamna Soludo cewa masu akidar ci gaba dole su yi aiki tare domin zurfafa dimokuradiyya, karfafa tsaro, da bunkasa tattalin arziki.
Ya ce:
“Ina tattaunawa kan sauye-sauyen da ake aiwatarwa, bukatar ci gaba da tafiya, da muhimmancin magance matsalar tsaro ta hanyar matakai da damar matasa.

Kara karanta wannan
Ana jita jitar rashin lafiyar Tinubu, Sanata ya fadi halin da Shugaban kasa ke ciki
“Gwamnatina za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da kowace jiha mai himma wajen ci gaban dan Adam, zamantakewa da tattalin arziki, domin ci gaban kasa baki daya.
“Za mu ci gaba da sa ran samun nasara a kasar mu ta Najeriya, domin tabbatar da dorewa da rabuwar arziki mai inganci a nan gaba.”
Gwamna Soludi ya fadi alakarsa da Tinubu
Gwamna Soludo ya samu halartar ganawar cikin tufafin gargajiya, yana dauke da hula mai alamar Tinubu, da hular da aka yi masa tambarin shugaban.
Bayan ganawar, Soludo ya bayyana wa manema labarai cewa tattaunawar ta kasance mai dadi, kuma shugaban kasa yana cikin koshin lafiya da walwala.
Ya kuma kara da cewa zumuncinsa da Tinubu ya kai sama da shekaru 20, ba kuma zai lalace saboda bambancin siyasa ba.
Tinubu ya nada mukamai a gwamnatinsa
Mun ba ku labarin cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sababbin kwamitocin lura da aikin hukumar sadarwa ta NCC da asusun USPF.

Kara karanta wannan
'Mun yi Allah wadai': Atiku ya fadi 'gaskiyar' abin da ya sa EFCC ta tsare Tambuwal
Idris Olorunnimbe ya zama shugaban majalisar da ke kula da NCC, yayin da Dr. Aminu Maida ya ci gaba a matsayinsa na mai gudanar da aikin hukumar.
Har ila yau, Ministan Sadarwa, Dr. Bosun Tijani, zai jagoranci kwamitin USPF, asusun da ke samar da kudin ayyukan sadawara.
Asali: Legit.ng