Gwamna Ya Koma ga Allah kan Rashin Lafiyar Mataimakinsa, Ya Jawo Aya a Al'kur'ani

Gwamna Ya Koma ga Allah kan Rashin Lafiyar Mataimakinsa, Ya Jawo Aya a Al'kur'ani

  • Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya bukaci al'ummar jihar su koma ga Allah, su roka wa mataimakinsa, Alhaji Aminu Alkali lafiya
  • Kefas ya jawo ayoyi daga Alkur'ani Mai Girma da Bayibul domin tunatar da al'umma muhimmancin taimakon juna da ceton ran Dan adam
  • Gwamnan ya tabbatar wa mazauna Taraba cewa idan lokaci ya yi da doka za ta yi aiki kan kujerar mataimakin gwamna, zai yi abin da ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Taraba - Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya koma tafarkin addini domin nema wa mataimakinsa, Alhaji Aminu Alkali, lafiya.

Mataimakin gwamnan Taraba, Aminu Alkali ya shafe watanni yana kwance ba shi da lafiya a wani asibiti a Abuja, lamarin da ya hana shi zuwa ofis.

Gwamnan Taraba, Agbu Kefas.
Gwamna Agbu Kefas ya roki al'ummar Taraba su sanya mataimakinsa cikin addu'a Hoto: Agbu Kefas
Source: Twitter

Gwamna Kefas ya roki al'ummar jihar Taraba su sanya mataimakinsa a addu'o'insu domin Allah ya tashi kafadunsa, kamar yadda Daily Trust ta rahoto

Kara karanta wannan

Zai koma APC ne? An ga gwamnan adawa ya sanya hula mai tambarin Tinubu a Aso Rock

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Kefas ya roki a yiwa mataimakinsa addu'a

Agbu Kefas ya bayyana cewa “wannan ba batu ne na siyasa ba, batu ne na ɗan Adam,” tare da kira ga mazauna Taraba da su roki Allah ya bai wa Aminu Alkali lafiya.

Mai girma gwamnan ya yi wannan roko ne yayin da yake jawabi kan rashin lafiyar mataimakinsa a bainar jama'a a karon farko, jiya Litinin a Jalingo.

Kefas ya ce:

“Na fahimci damuwarku, kuma ina so in yi magana da ku kai tsaye ba kawai a matsayina na gwamna ba, har a matsayina na ɗan adam da addini, ɗabi’a da zuciya ke jagoranta.”

Da yake kafa misali da rayuwarsa ta soja, Gwamna Kefas ya tunatar da muhimmancin hadin kai ba tare da la’akari da addini, kabila ko asali ba.

Ya yi kira ga jama’ar jihar Taraba da su yi wa Aminu Alkali addu’a, wanda ya kamu da rashin lafiya a lokacin da yake kan aiki, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya kawo tsarin da zai canza rayuwar 'yan daba a jihar Kano

Gwamna ya jawo ayoyi a Alkur'ani da Bayibul

Gwamna Kefas ya yi jawo ayoyi daga Bayibul da Alƙur’ani domin nuna muhimmancim taimakon juna da ceton rayuwar dan adam.

"A cikin Littafin Bayibul Mai Tsarki, Galatiana, 6:2 ta koya mana mu ‘taimaki juna a lokacin damuwa.’ A cikin Alƙur’ani, Suratul Ma’ida (5:32) tana tuna mana cewa ‘duk wanda ya ceci rai guda, kamar ya ceci al'umma ne.’”
"Yanzu, a lokacin da yake cikin buƙata, lokaci ne da za mu tsaya masa, mu masa addu’a, mu tallafa wa iyalinsa, mu nuna cewa a Taraba, muna fifita darajar dan adam kafin siyasa.
"Ba ni da wata manufa ta boye, idan lokaci ya yi da dole a yi aiki da kundin tsarin mulki kan kujerarsa ta mataimakin gwamna, ba zan yi jinkiri ba wajen yin hakan ta hanyar da ta dace."

- Agbu Kefas.

Mataimakin gwamnan jihar Taraba, Aminu Alkali.
Gwamnan Taraba ya ce zai yi abin da ya dace kan kujerar mataimakin gwamna Hoto: Aminu Alkali
Source: Twitter

Majalisa za ta tsige mataimakin gwamnan Taraba?

A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar dokokin Taraba ta ƙaryata jita-jitar shirin sauke Alhaji Aminu Alkali, wanda ya shafe tsawon lokaci yana jinya.

Kara karanta wannan

'Mun yi Allah wadai': Atiku ya fadi 'gaskiyar' abin da ya sa EFCC ta tsare Tambuwal

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Hon. Nelson Len ya ce babu wani shiri ko tunani da majalisar ke yi na tsige mataimakin gwamnan daga muƙaminsa.

'Dan Majalisar ya bayyana cewa ana sa ran Aminu Alkali zai koma bakin aikinsa bayan ya kammala samun sauki gaba ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262