Ma'aikata Sama da 3,000 na Fuskantar Hadari, Gwamnatin Tarayya na Iya Korarsu daga Aiki
- Gwamnatin tarayya ta sake sanya lokacin tantance wasu ma'aikata 3,598 saboda ba su samu zuwa tantancewar da aka yi a 2021 ba
- Hukumar kula da ma'aikata ta kasa ta bayyana cewa duk wanda ya gaza zuwa wannan tantancewar ya dauka ya rasa aikinsa
- A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce za a tantance ma'aikatan ne daga ranar 18 zuwa 28 ga watan Agusta, 2025
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ma'aikatan gwamnatin tarayya 3,598 na fuskantar barazanar kora saboda gaza gabatar da takardun daukarsu aiki.
Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (FCSC) ta umurci ma’aikata, wadanda suka gaza zuwa a tantance su a 2021, su gabatar da kansu domin tabbatar da sahihancin daukar su aiki.

Source: Twitter
Tribune Nigeria ta ce an tsara tantance ma'aikatan daga ranar 18 zuwa 28 ga watan Agusta, 2025, domin tabbatar da ingancin takardun shaidar ɗaukar aikinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar FCSC, duk wanda ya gaza halartar wannan tantancewa da aka shirya, za a ɗauka yana rike da jabun takardar ɗaukar aiki.
Hukumar ta umurci duka waɗanda abin ya shafa da su duba sunayensu a shafin intanet na FCSC, shafin intanet na Ofishin Shugaban Ma’aikatan Tarayya, da kuma allon sanarwa na ma’aikatunsu.
Gwamnati za ta sake tantance ma'aikata 3,598
Sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce:
“Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ta kammala shirye-shiryen gudanar da aikin sake tantance duk waɗanda suka gaza bayyana a lokacin aikin tantancewa na 2021.
"Wadanda lamarin ya shafa suna cikin ma’aikatan da hukumar ta ɗauka daga shekarar 2013 zuwa 2020.”
Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar korar ma'aikata
Hukumar ta ƙara da cewa duk ma’aikacin da ya gaza halarta, za a ɗauka yana da jabun takardar ɗaukar aiki kuma yana yin hakan ne da gangan domin guje wa tonon asiri.
Ana buƙatar waɗanda abin ya shafa su kawo takardun karatunsu na asali da kwafin su, ciki har da takardar ɗaukar aiki da ta ƙarin girma,

Kara karanta wannan
Kwana ya kare: Sanatan da ke shirin neman takarar shugaban kasa ya rasu a Colombia
Haka nan kuma an bukaci su je da takardar canjin matsayi, da kuma takardar albashi ta IPPIS na watan Yuli 2025.

Source: Twitter
Jerin ma'aikatun da abin ya shafa
Hukumar ta gargadi cewa ba za a sake ba da wani ƙarin lokaci ga waɗanda suka gaza halartar tantancewar a wannna karon ba.
- Ma’aikatun da suka fi yawan waɗanda abin ya shafa sun haɗa da:
- Ma’aikatar Yaɗa Labarai – ma’aikata 592
- Ma’aikatar Ilimi – ma’aikata 506
- Ma’aikatar Ƙwadago – ma’aikata 440.
Gwamnatin Tinubu za ta samar da ayyukan yi
A wani labarin, kun ji cewa ma'aikatar harkokin gidaje da raya birane ta ƙirƙiro shirin da zai samawa ƴan Najeriya sama da miliyan 2 ayyukan yi a Najeriya.
Ministan harkokin gidaje da raya birane, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ya ce gwamnati na da shirin samar da guraben ayyukan yi masu yawa a kowace karamar hukuma.
Ya ce za a gina gidaje guda 100 a kowace ƙaramar hukuma daga cikin ƙananan hukumomi 774 da ke fadin ƙasar nan, wanda hakan zai samar da dubban ayyuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
