"Allah Ya Taimake Ni": Babachir Lawal Ya Fadi Abin da Zai Hana Shi Aiki a Gwamnatin Tinubu
- Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya yi kalaman suka kan salon mulkin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- Babachir Lawal ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana nuna son kai tare da fifita 'yan kabilarsa a gwamnatinsa
- Ya nuna cewa da ace ya samu mukami a gwamnatin Tinubu, da tuni ya yi murabus don ba zai iya aiki a cikinta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, a ranar Litinin ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Babachir Lawal ya ce da yana cikin majalisar ministocin Shugaba Tinubu, da ba zai iya jure ci gaba da zama a cikinta ba.

Asali: Facebook
Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Babachir ba zai yi aiki da Tinubu ba?

Kara karanta wannan
'Mun yi Allah wadai': Atiku ya fadi 'gaskiyar' abin da ya sa EFCC ta tsare Tambuwal
A cewarsa, da tuni ya yi murabus da ace yana cikin gwamnatin Shugaba Tinubu.
“Na gode wa Allah da ban yi kuskuren shiga wannan gwamnati tun farko ba"
“Da ina cikin wannan gwamnati, watakila an riga an kore ni tun da dadewa, ko an kashe ni, ko kuma na yi murabus.”
- Babachir Lawal
Babachir Lawal ya bayyana cewa ba ya jin daɗin salon mulkin da Shugaba Tinubu ke gudanarwa.
Babachir ya soki gwamnatin Tinubu
Tsohon mamban na jam'iyyar APC ya zargi gwamnatin Tinubu da nuna son kai, inda ya yi nuni da irin nadin mukaman da shugaban kasan yake yi.
“Ba zan iya zuwa wani taro ba inda kashi 99 cikin 100 na mahalartansa duk Yarbawa ne. Sau da yawa za su kammala tattaunawa a harshensu, ni kuma na zauna kawai ina kallo."
"Lokacin da muke yakin neman zabe, bayan ya je Ogun ya ce ‘Emi lokan’, akwai wata dandalin goyon bayan Bola Tinubu da nake ciki."

Kara karanta wannan
"Ba Tinubu ba ne," Sakataren Gwamnatin Tarayya a mulkin Buhari ya fadi wanda ya ci zaben 2023
"Suka fara zaginmu, suna cewa 'yan Arewa jahilai ne. Sai na rubuta a wannan dandali cewa, waɗannan mutanen sune muke bukatar kuri’unsu.”
"Matsalar Yarbawa ita ce idan ka goyi bayansu suka ci nasara, suna nuna kamar sun maka wayau. Ba za su yi la'akari da goyon bayanka ba.”
- Babachir Lawal

Asali: Facebook
A yayin shirin, Babachir Lawal ya kuma soki wasu manufofin tattalin arzikin Tinubu, yana kokawa kan hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan.
Ya ambaci cire tallafin man fetur da aka yi a watan Mayun 2023, yana mai cewa har yanzu ‘yan Najeriya ba su ga ribar cire tallafin ba.
Ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da ci gaba da biyan tallafi duk da sanarwar shugaban cewa an cire shi.
Ina aka kwana kan rashin lafiyar Tinubu?
A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi martani kan rahotannin da ke cewa mai girma Bola Tinubu na fama da rashin lafiya.
Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya musanta cewa Tinubu na fama da ciwo, inda ya ba da tabbacin cewa lafiyarsa kalau.
Kalaman Onanuga dai na zuwa ne bayan an kwashe kwanaki ba a ga Shugaba Tinubu a cikin bainar jama'a ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng