Ana Murna Farashin Mai Ya Sauko a Duniya, An Samu Karin Kudin Litar Fetur a Najeriya
- Rahotanni sun bayyana cewa farashin gangar danyen mai ya sauko a kasuwar duniya bayan ganawa tsakanin Rasha da Amurka
- Sai dai gidajen mai a Legas, Ogun da wasu jihohi sun ƙara farashin fetur zuwa N900 da sama duk da raguwar farashin danyen mai
- Amma kungiyar PETROAN ta ce ana sa ran farashin fetur zai ragu a cikin makon nan idan kasuwar danyen mai ta ci gaba da sauka
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
JiharLagos –Gidajen mai a wasu sassa na ƙasar sun ƙara farashin litar fetur zuwa N900 zuwa sama duk da raguwar farashin danyen mai a kasuwar duniya tun ranar Lahadi.
Rahotanni sun ce gidajen mai mallakin NNPCL sun ƙara farashin fetur zuwa N900 a jihohin Legas da Ogun, duk da cewa farashin danyen mai ya faɗo daga kusan dala 69 zuwa dala 66 kowace ganga.

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wasu abokan hulɗar matatar Dangote, daga ciki har da Ardova da Heyden, sun ƙara farashin zuwa sama da N900 a kowace lita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farashin fetur ya bambanta a jihohin Najeriya
Rahoton ya ce kamfanin AP, wanda ke da alaƙa da matatar Dangote, ya sayar da fetur a N925 kowace lita a unguwar Mowe ta jihar Ogun, yayin da Heyden ya sayar a N910.
A ranar Litinin, gidajen mai da ke kan titin Legas zuwa Ibadan sun yi ciniki a farashi daban-daban, lamarin da ke nuni da cewa an samu karin farashin mai.
A makon da ya gabata, gidajen mai da dama a Legas, Ogun da wasu makwabtan jihohi sun sayar da fetur ƙasa da N900, yayin da farashin ya fi tsada a Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu da Arewacin kasar.

Source: Getty Images
Ranar Lahadi, kamfanin TotalEnergies ya sayar da fetur a N910, Asharami kuma ya sayar da kowace lita a kan N905.
A ranar Litinin, NIPCO da Fatgbems ba sun yi sauki, inda su ka sayar da lita a kan N890 da N892, yayin da Enyo ke sayarwa a N915 kowace lita.
A makon nan an saida gangar danyen mai a kan $66 wanda hakan ya nuna farashi ya karye da 5.7% a lokacin da Najeriya ta ci buri da kudin a kasafin 2025.
Matatar Dangote ta tabbatar da karin farashi
A ranar Juma’a, matatar Dangote ta tabbatar da ƙara farashin man da take sayarwa ga abokan huldarta zuwa N850 daga N820, ba tare da bayyana dalili ba.
Bayanan da aka fitar sun nuna cewa farashin fetur daga wurin dauko mai ya kai N855 kowace lita, inda Aiteo ke sayarwa a N850, Sobaz da Mainland kuma a N870.
Sauran sun haɗa da NIPCO Lagos (N852), Northwest (N860), Alkanes (N860), Ever (N863), TSL (N864), Pinnacle (N851.5), Menj (N852) da Sahara (N855).
Duk da karin farashin da aka samu, Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na ƙungiyar masu gidajen mai (PETROAN), Joseph Obele, ya bayyana cewa ana sa ran samun sauki.
Ya ce:

Kara karanta wannan
Sakkwato: Garuruwa sun zama kufai, 'yan ta'adda sun raba dubunnan mutane da gidansu
“A ƙarshen makon da ya gabata, farashin danyen mai ya tashi, don haka matatun mai suka kara farashi. Bayan kwana kaɗan, farashin ya ragu sakamakon taron da aka yi tsakanin Trump da jakadan Rasha.”
“Kafin ko zuwa ranar Talata, muna sa ran ganin saukar farashin fetur.”
NNPCL ya canza farashin man fetur
A wani labarin, kun ji cewa a yayin da ƴan Najeriya ke ci gaba da fama da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa, Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya sake ƙara farashin litar fetur.
A ranar Litinin, 4 ga watan Agusta, 2025, gidajen mai mallakin NNPCL da ke jihar Legas sun ƙara farashin lita daga N865 zuwa N915, wanda ke nufin ƙarin N50 a kowace lita.
A babban birnin tarayya Abuja, gidajen mai na NNPCL sun ƙara farashin lita daga N890 zuwa N955, wanda ke nuna an samu ƙarin N65 lamarin da ya tayar da ce-ce-ku-ce tsakanin direbobi.
Asali: Legit.ng
