"Daga Ciwon Haƙori," Pantami Ya Faɗi Yadda Ajalin Tsohon Shugaba Buhari Ya Riske Shi

"Daga Ciwon Haƙori," Pantami Ya Faɗi Yadda Ajalin Tsohon Shugaba Buhari Ya Riske Shi

  • Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya bayyana cewa kafin rasuwar Muhammadu Buhari, babu alamar cutar ajali a tare da shi
  • Isa Pantami ya bayyana cewa Buhari ya tafi Landan da kwarinsa domin a duba masa hakori da ya dan dame shi, amma ba wata kwakkwarar cuta ba ce
  • Babban malamin addinin ya ce rasuwar tsohon shugaban kasa ta faru ne saboda lokaci ya yi, ba saboda wani ciwo da ya tsananta ko ya shiga damuwa ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Tsohon Ministan Sadarwa a gwamnatin Muhammadu Buhari, Farfesa Isa Ali Pantami, ya bayyana yadda ciwon ajali ya kama tsohon shugaban kasa.

Ya ce babu wanda ya kawo wa Muhammadu Buhari rasuwa a lokacin da ya koma ga Mahaliccinsa a ranar 13 ga watan Yuli, 2025.

Kara karanta wannan

Kafin ya mutu, tsohon minista Audu Ogbeh ya hango masifar da ke tunkaro Najeriya

Farfesa Isa Ali Pantami da Muhammadu Buhari
Pantami ya ce ba a kawo wa Buhari mutuwa ba Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

A wata hira da aka wallafa a shafin Facebook na Premier Radio, Farfesa Pantami ya bayyana cewa, duk da cewa idan mutuwa ta zo babu dabara, rasuwar tsohon shugaban kasar ta girgiza su matuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Muhammadu Buhari ya tafi Landan

Farfesa Pantami ya ce ƙaramin ciwo ne ya kai Muhammadu Buhari Landan, kuma babu wata alamar ciwon ajali a tattare da shi a lokacin da ya bar Najeriya.

Ya ce:

“A lokacin da ya rasu, ba ma tsammanin hakan saboda babu wata jinya da ke nuna haka. Gabannin ya bar Najeriya zuwa Landan, kasa da awa 12 kafin tafiya ina tare da shi, kuma a wannan tarayya kila na kwashe awa shida ina tare da shi".
“Har ga Allah, babu wani abu da ke nuna cewa yana da wata damuwa ta rashin lafiya. Shi ma kansa bai so ya je Landan a duba lafiyarsa ba. Abin da kawai ya kai shi, shi ne ya matsu likitansa ya duba hakorinsa. Bayan wannan, bai da wata damuwa. Dama yana zuwa daga lokaci zuwa lokaci ana duba hakorinsa.”

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi babban rashi, tsohon ministan Buhari, Audu Ogbeh ya rasu

Pantami: ‘Asibitin Najeriya ya tura Buhari Landan’

Pantami ya ce ba haka kawai tsohon shugaban kasa ke tafiya Landan ba. Ya bayyana cewa wani asibitin Najeriya da ke duba lafiyarsa ne ya aike shi ganin likitansa a Landan kan matsalar hakorinsa.

Farfesa Pantami ya ce:

“An fara duba shi a Najeriya, sai aka tura shi wajen wani likita da yake ziyarta a Landan. Wannan kawai ne ya kai shi can. Amma kamar yadda muka sani, idan ajali ya zo babu dabara. Idan lokaci ya yi dole a tafi. Saboda haka, rasuwarsa lokaci ne ya yi, ba wai wata cuta ce ta tsananta gare shi ba.”
Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari
Ciwon hakori ne ya kai Buhari Landan Hoto: Bashir Ahmad
Source: Getty Images

Tsohon ministan ya ce a shekarar 2017 ne aka yi tsammanin Buhari zai rasu saboda tsananin jinya, amma Allah Ya ba shi lafiya. Ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa.

Yadda Buhari ya nada Pantami Minista

A baya, mun wallafa cewa tsohon Minista, Farfesa Isa Ali Pantami ya fadi yadda Muhammadu Buhari ya naɗa shi manyan mukamai biyu a gwamnatinsa ba tare da ya san za a yi hakan ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi martani mai zafi, ta ce ana zuzuta batun yunwa a Najeriya

A bidiyon, Pantami ya bayyana cewa ya fara haɗuwa da Muhammadu Buhari ne a birnin Madina kafin nadin da ya samu a matsayin shugaban Hukumar NITDA.

Ya ce wannan ganawa ta kasance ta musamman, domin daga baya sai ya samu labarin cewa an naɗa shi shugaban hukumar ba tare da wani shirye-shirye na musamman daga gare shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng