Mai Hidimar Kasa da Ta Caccaki Tinubu Ta Zargi NYSC da Jefa Ta a Matsala
- Rita Uguamaye daliba mai hidimar kasa a jihar Legas ta shiga matsala, inda ta yi zargin an sako ta a gaba saboda sukar gwamnatin Bola Tinubu
- Ta zargi hukumar NYSC da hana ta takardar kammala hidimar kasa duk da cewa ta kammala shekara guda da kowane dalibi ke yi
- A martanin NYSC, ta ce an tsawaita shekarar hidimar kasar Rita saboda kin yin tantancewar Afrilu, ba saboda maganganunta kan gwamnati ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Rita Uguamaye, ta jawo sabon cece-kuce bayan ta zargi hukumar hidimar kasa ta NYSC da hana ta takardar kammala bautar kasa.
Rita, wacce aka fi sani da Raye, ta yi hidimar ƙasa ne a Legas kuma ta fara shahara a watan Maris lokacin wani bidiyo da ta yi na caccakar gwamnatocin tarayya da Legas.

Asali: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa a cikin bidiyon, ta koka kan halin matsin tattalin arzikin Najeriya da hauhawar farashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta bayyana shugaban ƙasa Bola Tinubu a matsayin mugun shugaba, ta kuma zargi gwamnatin tarayya kan jinkirin aiwatar da sabon alawus na masu hidimar 'kasa.
'Yar bautar kasa ta zargi NYSC da take hakkinta
Premium Times ta ruwaito cewa a watan Yuni, rahotanni sun yi zargin cewa NYSC ta tsawaita shekarar bautar Raye a matsayin hukunci saboda maganganunta, zargin da hukumar ta karyata.
A ranar Asabar, Raye ta ce an hana ta karɓar takardar kammala hidimar kasa lokacin da ta je tare da abokan karatunta domin karɓar takardar.
A cewarta, jami’an NYSC sun yi zargin cewa ba ta kammala shigar da bayananta na watan Afrilu ba, abin da ta ce ba gaskiya ba ne.
Martanin hukumar NYSC ga Rita Uguamaye
A cikin wata sanarwar da NYSC ta fitar, ta karyata cewa ta hana Raye takardar kammala hidimar kasa saboda maganganunta kan gwamnati.

Asali: Facebook
Sanarwar ta ce:
“Rita tana cikin jerin ‘yan hidimar ƙasa 131 da aka hana su takardar kammalawa saboda kin halartar tantancewar watan Afrilu 2025. An tsawaita shekarar bautarta da watanni biyu bisa dokokin NYSC.”
NYSC: 'Yan gwagwarmaya, manyan 'yan siyasa sun magantu
Maganganunta sun jawo martani daga ‘yan siyasa, ‘yan gwagwarmaya da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya bayyana lamarin a matsayin abin ddamuwa matuka.
Lauyan kare haƙƙin bil’adama kuma Babban Lauya (SAN), Femi Falana, ya bayyana abin a matsayin ƙeta doka, yana mai cewa:
“Tunda Najeriya tana karkashin gwamnatin dimokuraɗiyya, doka ta kare haƙƙin Rita Uguamaye na yin sukar gwamnati a ƙarƙashin Sashe na 39 na Kundin Tsarin Mulki.”
Kungiyar Amnesty International ma ta la’anci abin da aka yi zargin da NYSC ta aikata, tana kiran sa “ƙin jurewa masu adawa” da kuma tauye ‘yancin faɗin albarkacin baki.
Sarkin Musulmi ya gwangwaje 'yan NYSC

Kara karanta wannan
Ana batun yunwa, gwamnatin Tinubu ta fitar da ton 42,000 na hatsi a raba wa jihohi
A wani labarin, kun ji cewa wasu ‘yan bautar ƙasa biyu na rukunin Batch sahu na biyu da aka tura jihar Sakkwato sun samu lambar yabo daga fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi.
Fadar Sarkin Musulmi ƙarƙashin Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar III ta bai wa matashin namiji da mace, waɗanda ke yi wa ƙasa hidima a jihar, kyaututtuka masu tsoka.
Kyautar ta haɗa da talabijin na bango da kuma kuɗi N100,000 kowannensu a matsayin yabo ga halayensu na kirki da jajircewar yin aiki tukuru a lokacin hidimar ƙasa.
Asali: Legit.ng