Gwamna Ya Runtuma Kora, Ya Sallami Kwamishinoni da Masu ba Shi Shawara
- Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya raba wasu daga cikin jami'an gwamnatinsa daga mukamansu
- Biodun Oyebanji ya sanar da rushe majalisar zartarwar jihar tare da korar wasu daga cikin kwamishinoninsa da masu ba shi shawara na musamman
- Gwamnan ya yi fatan alheri ga wadanda suka rasa mukamansu tare da umartarsu, su mika ragamar mulki ga manyan sakatarori
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Ekiti - Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya sallami wasu dava cikin kwamishinoni da jami'an gwamnatinsa.
Gwamna Biodun Oyebanji ya rusa majalisar zartarwar jihar nan take ba tare da ba ta lokaci ba.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce sakatariyar gwamnatin jihar, Farfesa Habibat Adubiaro, ce ta sanar da rushe majalisar zartarwar a cikin wata sanarwa da ta fitar a daren Lahadi, 10 ga watan Agustan 2025.
Gwamna Biodun Oyebanji ya kori kwamishinoni
Korar da gwamnan ya yi ta shafi wasu kwamishinoni da manyan masu ba da shawara na musamman ga Gwamnatin Biodun Oyebanji.
An umarci kwamishinoni da manyan masu ba da shawara na musamman da abin ya shafa, su mika mulki ga babban sakatare ko kuma ma’aikacin gwamnati mafi girma a mukami a kowace ma’aikata.
Gwamna Biodun Oyebanji ya gode wa mambobin majalisar zartarwa da suka kammala wa’adinsu tare da yi musu fatan alheri a ayyukan da za su gudanar a nan gaba, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Gwamna ya dagawa wasu jami'ai kafa
Sanarwar ta ci gaba da cewa korar ba ta shafi kwamishinan shari'a da sauran wasu kwamishinoni ba.
"Rushewar ba ta shafi Antoni janar kuma Kwamishinan shari’a ba. Haka kuma, ba ta shafi Kwamishinan lafiya da ayyukan jin kai, kwamishinan harkokin noma da samar da Abinci."
"Kwamishinan ilimi, kwamishinan ayyuka, kwamishinan harkokin kasuwanci, zuba jari, masana’antu da kungiyoyin hada-hadar kasuwanci."
"Mai ba da shawara na musamman kan ilimi da mai ba da shawara na musamman kan filaye, safiyo da tsarin e-GIS."
“Haka kuma, dukkan shugabanni da suke mambobin majalisar zartarwa ta jihar za su ci gaba da rike mukamansu."
"Wadannan sun hada da shugaban ofishin OTSD, shugaban SDGs da kula da ayyuka da shugaban hukumar BPP."
- Farfesa Habibat Adubiaro

Source: Twitter
Karanta wasu karin labaran kan gwamnan Ekiti
- "Babu wanda zai canza yin Allah," Gwamna ya faɗi saƙon da ake turo masa a waya
- Gwamna ya sanar da sabon albashin da zai fara biyan ma'aikata, ya yi karin fansho
- Gwamna ya naɗa wanda zai maye gurbin shugaban alƙalai awanni bayan ya rasu
- Ana cikin halin kunci, Tinubu ya ware gwamna 1 a Najeriya, ya yaba masa
Gwamna Oyebanji ya nada shugaban ma'aikata
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadar gwamnati.
Gwamna Biodun Oyebanji ya nada Oyeniyi Adebayo a matsayin wanda zai rike kujerar shugaban ma'aikatan fadar.gwamnatin jihar.
Nadin da aka yi masa na zuwa ne bayan an sauya masa mukaminsa na kwamishinan kudi da tsare-tsaren tattalin arziki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

