Shugaba Tinubu Na Fama da Rashin Lafiya? Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Bayani

Shugaba Tinubu Na Fama da Rashin Lafiya? Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Bayani

  • Rashin ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bainar jama'a ya sanya an fara magana kan halin da lafiyarsa take ciki
  • Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa shugaban kasan na fama da rashin lafiya kuma ana shirin kai shi kasar waje domin kula da lafiyarsa
  • Sai dai, fadar shugaban kasa ta yi martani kan maganganun da ke nuna cewa mai girma Bola Tinubu na fama da rashin lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi martani kan batun cewa mai girma Bola Tinubu ba shi da lafiya.

Fadar shugaban kasan ta karyata jita-jitar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana fama da rashin lafiya.

Ana magana kan rashin lafiyar Tinubu
Fadar shugaban kasa ta ce Tinubu lafiyarsa lau Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Rahoton cibiyar ICIR ya ambato wasu majiyoyi sun bayyana cewa ana shirin tura shugaban ƙasan ƙasashen waje domin duba lafiyarsa cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Legas zai bar tafiyar Tinubu ya koma ADC? Ambode ya fayyace gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana cewa Bola Tinubu ya kwanta ciwo

Bisa bayanan da cibiyar ta tattara, an ce shugaban ƙasa ya kwanta rashin lafiya tsawon wasu kwanaki, lamarin da ya sa bai halarci wasu manyan tarurrukan ƙasa ba.

A sakamakon haka, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya wakilce shi a wasu muhimman ayyuka na gwamnati.

Haka kuma, majiya daga Aso Rock da cibiyar ta ambata ta ce tun farkon makon da ya gabata, an soke wasu daga cikin shirye-shiryen ayyukan da aka tsara wa shugaban ƙasa.

Gani na karshe dai da aka yi wa Tinubu a bainar jama'a shi ne a ranar Juma'a 1 ga watan Agustan 2025, inda ya halarci bude wani taro.

Me fadar shugaban kasa ta ce kan lafiyar Tinubu?

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da bayanai, Bayo Onanuga, ya shaidawa cibiyar cewa jita-jita ce kawai kuma shugaban kasan yana aikinsa.

Kara karanta wannan

Davido: Mawakin Najeriya ya yi auren kece raini, ya kashe sama da Naira biliyan 5

"Mutane suna ta gaya muku jita-jita marasa tushe iri-iri. A ranar 5 ga watan Agusta yana ofis dinsa. Na je na gan shi. Ya zo ofis ya yi aiki."

- Bayo Onanuga

A daren jiya, jaridar Daily Trust ta tuntubi Onanuga kai tsaye, inda ya yi watsi da jita-jitar cewa shugaban ƙasa na fama da rashin lafiya.

Onanuga ya ce lafiyar Tinubu lau
Fadar shugaban kasa ta ce Tinubu na cikin koshin lafiya Hoto: @aonanuga1956
Asali: Facebook

Game da dalilin da ya sa shugaban ƙasa bai halarci wani taron bainar jama’a tun makon da ya gabata ba, Onanuga ya bayyana cewa shugaban ƙasa na da ‘yancin yin aiki daga gida.

"Babu wata matsala da shugaban ƙasa, yana cikin koshin lafiya. Yana iya yanke shawarar yin aiki daga gida. Yana iya yin aiki daga duk inda ya ga dama. Ina tabbatar muku babu wata matsala da shugaban ƙasa."

- Bayo Onanuga

Ya kamata Tinubu ya samu goyon bayan Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigon jam'iyyar APC a jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya bukaci manyan 'yan siyasar Arewa su goyawa mai girma Bola Tinubu baya.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa ta dura kan Obasanjo, ta yi masa gori bayan shekaru 8 a mulki

Oyintiloye ya bayyana cewa shugaban kasan ya gudanar da ayyukan da ya kamata su sanya a mara masa baya kan tazarcensa a shekarar 2027.

Hakazalika ya yi kira ga shugabannin Arewa da ka da su bari wasu tsiraru su rika bata sunan shugaban kasan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng