Jami'an 'Yan Sanda Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga a Katsina, an Ceto Mutane

Jami'an 'Yan Sanda Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga a Katsina, an Ceto Mutane

  • Jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Katsina sun samu nasarar dakile wani mugun nufi da 'yan bindiga suka shirya
  • Sun dai samu nasarar ne bayan samun rahoton cewa 'yan bindiga sun tare wasu matafiya da ke kan hanyar Funtua zuwa Gusau
  • Bayan an yi artabu tsakanin jami'an tsaron da 'yan bindiga, an samu nasarar kubutar da mutanen da aka yi yunkurin yin garkuwa da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa ta tarwatsa yunkurin 'yan bindiga na yin garkuwa da mutane.

Jami'an rundunar 'yan sandan sun kuma ceto wasu mutane uku ba tare da wani rauni ba a Marabar Bangori, a kan hanyar Funtua zuwa Gusau.

'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga
'Yan sanda sun tarwatsa shirin 'yan bindiga a Katsina Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ƴan bindiga sun kai hari 'Gidansu Atiku,' sun yi garkuwa da mata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun tare matafiya

Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne kusan karfe 11:00 na dare, a ranar Asabar, 9 ga watan Agustan 2025.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka yi shirin kai farmakin, inda suka yi wa wata mota kirar farar Golf 3 Wagon mai lambar rajista BWR 104 HE kwanton-bauna.

Motar, wacce ke da direbanta mai suna Sadi Ahmed, mai shekara 45, na dauke da wasu fasinjoji biyu, Ibrahim Umar, mai shekara 40, wanda aka fi sani da Dan’iya, da kuma Babangida Yusuf, mai shekara 45 dukkansu ‘yan asalin garin Yankara.

Bisa ga bayanan da aka samu, motar na dauke da kayan tumatir daga Funtua zuwa Yankara lokacin da aka kai harin.

'Yan sanda sun kai dauki

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, bayan samun kiran gaggawa, DPO ya tattara tawagar sintiri da ke amfani da motar sulke ta musamman (APC) zuwa wurin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun ragargaji 'yan bindiga a Bauchi, an kashe miyagu

Da isarsu wurin, jami’an ‘yan sandan suka shiga fafatawa da ‘yan bindigan ta hanyar dabarun musayar wuta, wanda hakan ya tilasta wa maharan tserewa zuwa wani wuri da ba a sani ba.

'Yan sanda sun samu nasara kan 'yan bindiga
'Yan sanda sun ragargaji 'yan bindiga a Katsina Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jami'an 'yan sandan sun samu nasarar ceto mutanen uku da aka yi niyyar yin garkuwa da su, ba tare da wani daga cikinsu ya samu rauni ba.

Rundunar ‘yan sandan ta jaddada kudirinta na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da yin kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayar da bayanai cikin lokaci, domin tabbatar da cewa irin wannan hari bai samu nasara ba a nan gaba.

Abin a yaba ne

Sahabi Abdulrahman ya shaidawa Legit Hausa cewa nasarar da jami'an tsaron suka samu abin a yaba ne.

"Wannan nasarar abin a yaba ne muna fatan za su ci gaba da kokari wajen kawo karshen ayyukan 'yan bindiga."
"Lamarin na 'yan bindiga akwai ban tsoro yadda suke cin karensu babu babbaka, Allah dai ya kawo mana dauki kawai."

- Sahabi Abdulrahman

'Yan bindiga sun kai hari a Katsina

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare matafiya a hanya, an yi awon gaba da fasinjoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

'Yan bindigan sun kai harin ne a kauyen 'Gidansu Atiku' da yamma inda suka aikata ayyukan ta'addanci.

Miyagun sun yi awon gaba da wasu mata guda biyu tare da shanu a harin da suka kai cikin kauyen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng