Jigawa: Wanda Ake Zargi da Kashe Jami'in NSCDC Ya Yi Mummunan Ƙarshe bayan Cafke Shi

Jigawa: Wanda Ake Zargi da Kashe Jami'in NSCDC Ya Yi Mummunan Ƙarshe bayan Cafke Shi

  • Wani mutum mai shekara 45 da ake zargi da kisan jami’in NSCDC ya rasu bayan faduwa daga mota
  • Kakakin NSCDC, ASC Badaruddeen Tijjani, ya ce wanda ake zargin ya tsere daga ankwa yayin da ake tafiya da shi
  • An garzaya da shi Asibitin Dutse amma likita ya tabbatar da mutuwarsa, yayin da hukumar ta sha alwashin ganin an samu adalci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dutse, Jigawa - Wani mutum mai shekara 45 da ake zargi da hannu wajen kisan jami’in Hukumar NSCDC ya mutu sanadin fadowa daga mota a jihar Jigawa.

Majiyoyi suka ce mutumin ya mutu ne bayan faduwa daga mota yayin da ake cikin tafiya da shi zuwa ofishinsu domin ci gaba da bincike.

Ana fargaban wani da ake zargin ya kashe jami'in NSCDC ya mutu
Wanda ake zargi da kashe jami'in NSCDC ya mutu. Hoto: NSCDC.
Asali: Twitter

NSCDC: Wanda da ake zargi da kisa ya mutu

Kara karanta wannan

Davido: Mawakin Najeriya ya yi auren kece raini, ya kashe sama da Naira biliyan 5

Wannan bayani ya fito ne daga bakin kakakin hukumar a jihar, ASC Badaruddeen Tijjani, ranar Asabar 9 ga watan Agustan 2025 a Dutse, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito cewa an kashe jami’in ne a kasuwar Shuwarin, yayin da yake kan aikinsa na wani bincike lokacin da abin ya afku.

Yadda aka hallaka jami'in hukumar NSCDC

Mamacin, Bashir Adamu-Jibril, wanda ke da mukamin 'Superintendent of Corps', ya yi aiki a sashen leken asiri da bincike na hukumar kafin rasuwarsa.

Ana zargin masu kisan, wadanda ake ganin yan sara ne, sun sare shi da adda, har suka yanke bayan kansa cikin mugun yanayi.

Tijjani ya bayyana cewa wanda ake zargi, mazaunin Shuwarin, an kama shi ne ranar Alhamis 7 ga watan Agustan 2025 bayan samun sahihin bayani kan hannunsa a lamarin.

Ana zargin wanda ya kashe jami'in NSCDC ya mutu
Hukumar NSCDC ta ce wanda ake zargin ya kashe jami'inta ya mutu. Hoto: Legit.
Asali: Original

Wani da NSCDC ta kama ya mutu a hanya

Ya ce an yi nasarar cafke shi ne a ranar 7 ga watan Agusta a garin Shuwarin, cikin karamar hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare matafiya a hanya, an yi awon gaba da fasinjoji

Hukumar ta sanar da cewa:

“Amma, yayin jigilar shi zuwa ofishinmu, sai ya kwance kansa daga ankwa, ya dura daga mota don tserewa.
“Ya samu munanan raunuka, aka garzaya da shi Asibitin Dutse, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa a lokacin.”

Kakakin hukumar NSCDC ya jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da aiki tukuru domin ganin an samu adalci ga mamacin da kuma tsare doka da oda.

Ya kuma bukaci al'umma su kwantar da hankali ba tare da ɗaukar wata doka a hannu ba domin ci gaba da bincike kan ainihin wadanda suka aikata laifin.

Jigawa: Mutane sun mutu a hatsarin jirgin sama

A baya, kun ji cewa wani hadari ya auku a Jihar Jigawa inda yara mata takwas suka mutu bayan jirgin ruwa ya kife a kogin Zangwan Maje a karamar hukumar Taura.

Yaran 15 ne ke cikin jirgin lokacin da hadarin ya auku da misalin karfe 8:15 na dare, yayin da wata guguwa mai karfi ta tashi wanda shi ne sanadinsu.

Jirgin ruwa ya kife ne sakamakon ambaliya da iska mai ƙarfi, an ceto yara bakwai, sai kuma aka tono gawarwakin yara matan takwas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.