'Yan Sandan Kano Sun Fara Binciken Kisan 'Ɗan Fashi' bayan Koken Uwarsa
- Rundunar ‘yan sandan Kano ta fara bincike kan koken wata uwa da ta zargi mazauna Unguwar Kwalwa da kashe ɗanta
- Jama'an gari sun ji kukan neman ɗaukin makwabcinsu, inda nan take aka kai masau taimakon gaggawa
- A nan ne aka kashe Mas'ud Dahiru bayan an ruwaito cewa ya ci na jaki tare da abokan fashinsa a garin na kano
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rundunar ƴan sandan Kano ta bayyana cewa ta fara bincike kan koken wata uwa, wadda ta zargin yan unguwa da kashe ɗanta.
Tana ganin mazauna Unguwar Kwalwa a ƙaramar hukumar Birni sun kashe ɗanta, Mas’ud Dahiru, wanda ake zargi da fashi da makami.

Asali: Facebook
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da wannan lamarisaƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fashi da makami: 'Yan Kano sun yi kukan kura
Lamarin ya faru ne a ranar 3 ga Agusta, 2025, da misalin 2:00 na dare, inda Mas’ud Dahiru, mai shekaru 24, ya shiga gidan Musa Hassan da nufin yin fashi.
A cewar ‘yan sanda, Mas’ud ya yi ƙoƙarin soka wa matar gidan wuka, amma ɗan gidan, Muhammad Musa, mai shekaru 18, ya taka masa burgi.
Sannan Mas’ud ya soka wa Muhammad wuka a baya da fuska, sai dai yana nan da ransa bai samu matsala ba
Daga nan ne mutanen gidan su ka yi kururuwar neman taimako, inda jama’a suka cafke Mas’ud tare da wani abokinsa mai shekaru 38, Alhaji Haruna, suka yi musu dukan kawo wuƙa.
Daga bisani aka kai su asibitin Murtala Muhammed, inda aka tabbatar da mutuwar Mas’ud, yayin da abokinsa da wanda ya jikkata ke ci gaba da jinya.
'Yan sandan Kano na bincike mutuwar
Kwamishinan ‘yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori (PhD), ya tabbatar wa jama’a cewa za a zurfafa bincike na gaskiya da adalci.
Legit Hausa ta fahimci cewa wata innar wannan yaro da ake zargi da laifin kisa ta yi kokarin wanke shi, duk da ta yarda cewa sun shiga satar kudi ne a gidan.
Wasu mazauna sun tofa albarkacin bakinsu kan iƙirarin uwar marigayin.
Aminu Abdullahi Ibrahim ya ce:
“Na daɗe ban ga son zuciya irinta ba.”

Asali: Facebook
Hadiza ta ce:
“Ita kanta ma ta san ɓarawo ne, kuma shi ɗan da ya shiga da niyyar sata, ai ya san komai zai iya faruwa da shi.”
Hadiza na ganin dai bai fi rai ba, kuma kisan Mas'ud kamar rage mugun iri ne a cikin al'ummar da ke fama da fashin.
Ƴan sandan Kano sun fara bincike
A baya, kun ji cewa Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta fara bincike kan kisan Sadiq Shu’aibu, wanda aka fi sani da Sadiq Gentle, wanda jami'in gwamnati ne.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba: 'Yadda Sadiq Gentle ya cika alhali muna shirin kai shi asibitin kasar waje'
A cewar ‘yan sanda, lamarin ya auku ne a ranar 4 ga Agusta, 2025, 7:30 na yamma, lamarin da ya jefa mazauna jihar a cikin ruɗani da alhinin rashin Sadiq.
An garzaya da shi asibitin kwararru na Murtala Muhammed don samun kulawa, amma ya rasu a ranar 7 ga Agusta, 2025 ana shirin fitar da shi turai don neman lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng