'Yadda Buhari Ya Hana Tazarcen Obasanjo Karo na 3 a 2006'

'Yadda Buhari Ya Hana Tazarcen Obasanjo Karo na 3 a 2006'

  • Tsohon Shugaban hukumar VON, Osita Okechukwu ya tuna baya kan neman wa'adin mulki na uku da Olusegun Obasanjo ya nema a 2006
  • Osita Okechukwu ya bayyana cewa marigayi Muhammadu Buhari ya taka muhimmiyar rawa wajen hana aukuwar hakan
  • 'Dan siyasar ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa ya tsaya tsayin daka wajen ganin shirin na Obasanjo bai yi nasara ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon Darakta Janar na hukumar VON, Osita Okechukwu, ya yi magana kan rawar da Muhammadu Buhari ya taka wajen hana tazarcen Olusegun Obasanjo karo na uku.

Osita Okechukwu ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taka muhimmiyar rawa wajen hana Olusegun Obasanjo cimma burin neman wa’adi na uku a shekarar 2006.

Buhari ya kawo cikas ga tazarcen Obasanjo
Buhari ya tsaya tsayin daka kan hana tazarcen Obasanjo a 2006 Hoto: @MBuhari, @Oobasanjo
Asali: Twitter

Jaridar Tribune ta rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Osita Okechukwu ya sanyawa hannu.

Kara karanta wannan

'Rasuwar Buhari ba za ta kawo cikas ba tazarcen Tinubu ba a 2027', Sanata Adeyeye

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Buhari ya kawo cikas ga Obasanjo

Osita Okechukwu ya bayyana cewa Buhari ya gudanar da muhimman tarurruka na dabarun siyasa tare da shugabanni da mambobin majalisar dokoki ta ƙasa, domin tabbatar da cewa ‘yan majalisar ba su amince da shirin wa’adi na ukun ba.

"Tsayin dakan Buhari, tare da gudanar da muhimman tarurruka da mambobin majalisar dokoki ta kasa, sun tabbatar da cewa ba a bari shirin wa’adi na uku ya samu nasara ba."
"Buhari ya ƙarfafa goyon bayan tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani, da kuma shugaban majalisar wakilai na wancan lokaci, Aminu Masari, domin su gane muhimmancin mutunta muradun ‘yan Najeriya."
"Wannan mataki ya zama babban dalilin da ya kawo ƙarshen shirin kafa jam’iyya ɗaya tilo a ƙasar nan, duk da zargin bayar da cin hancin Naira miliyan 50 ga kowane ɗan majalisar dokoki."
"Ana tuna yadda Buhari ya tsaya tsayin daka bayan ya samu labarin cewa Obasanjo yana shirya neman wa’adi na uku a 2006."

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa ta dura kan Obasanjo, ta yi masa gori bayan shekaru 8 a mulki

"Wannan shi ne ya kawo ƙarshen shirin kafa jam’iyya ɗaya, duk da zargin bayar da Naira miliyan 50 ga kowane ɗan majalisar dokoki.”

- Osita Okechukwu

Buhari ya hana tazarcen Obasanjo
Buhari ya kawo cikas ga tazarcen Obasanjo a 2006 Hoto: @Mbuhari
Asali: Twitter

Marigayi Muhammadu Buhari ya samu yabo

Jigon na jam’iyyar APC ya bayyana cewa wannan matakin na Buhari ya hana kafa tsarin jam’iyya ɗaya, abin da ya zama muhimmin lamari a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya, rahoton Daily Post ya tabbatar.

"Wannan taƙaitaccen nazari ne kan yadda Buhari ya yi amfani da dabarunsa wajen dakatar da shirin kafa jam’iyya ɗaya a ƙasar nan."

- Osita Okechukwu

Rasuwar Buhari ba za ta hana tazarcen Tinubu ba

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanata a jihar Osun, Dayo Adeyeye, ya bayyana cewa rasuwar Muhammadu Buhari ba za ta kawo cikas ga tazarcen Shugaba Bola Tinubu ba a zaben 2027.

Tsohon sanatan ya bayyana cewa Shugaba Tinubu baya bukatar farin jinin Buhari kafin ya lashe zabe domin ya samu karbuwa a dukkanin yankunan kasar nan.

Hakazalika ya nuna cewa ko a zaben shugaban kasa na shekarar 2023, ba tasirin Muhammadu Buhari ba ne ya kawo nasarar mai girma Bola Tinubu ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng