Rundunar Ƴan Sandan Kano Ta Fara Binciken Kisan Hadimin Gwamna, Sadiq Gentle

Rundunar Ƴan Sandan Kano Ta Fara Binciken Kisan Hadimin Gwamna, Sadiq Gentle

  • Rundunar ‘yan sandan Kano ta fara binciken kisan Sadiq Gentle, hadimin Gwamna Abba Kabir Yusuf, bayan harin da aka kai masa
  • Maharan sun soka wa Sadiq Gentle wuƙa sannan suka yi masa fashi, inda daga bisani ya rasu a gadon asibiti da ake ƙoƙarin ceton ransa
  • Wasu daga cikin al’umma sun roƙi gwamnati da ‘yan majalisa su ɗauki matakai masu tsauri kan ‘yan daba da masu kwacen waya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce tana binciken harin da ya yi sanadin rasuwar Sadiq Gentle, hadimin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Rundunar ta bayyana cewa a ranar 4 ga Agusta, 2025, misalin ƙarfe 7:30 na yamma, wasu da ba a san su ba su ka kai farmaki gidan Sadiq Shu’aibu, wanda aka fi sani da Sadiq Gentle.

Kara karanta wannan

'Yan sandan Kano sun fara binciken kisan 'ɗan fashi' bayan koken uwarsa

Marigayi hadimin Gwamnan Kano, Sadiq Gentle
Yan sanda sun fara binciken kisan hadimin Abba Hoto: Sadiq Gentle
Source: Facebook

Wannan na kunshe a sakon da Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook da yammacin Asabar, 9 ga watan Agusta, 2025.

Yadda ɓata-gari su ka hallaka Sadiq Gentle

Rundunar ‘yan sandan ta ƙara da bayyana cewa ɓata-garin sun soka wa Sadiq Gentle wuƙa sannan su ka yi masa fashi.

An garzaya da shi asibitin kwararru na Murtala Muhammed don samun kulawa, amma ya rasu a ranar 7 ga Agusta, 2025.

Lamarin ya daga hankulan mazauna Kano, sai dai rundunar ta bayar da tabbacin cewa za ta yi cikakken bincike domin ɗaukar matakin shari'a.

Roƙon jama'ar Kano ga ƴan sanda da gwamnati

Mutanen da su ka bibiya saƙon SP Abdullahi Haruna Kiyawa sun bayyana fatan a samu nasara a binciken da za a yi.

Guda daga cikin waɗanda su ka magantu ya yi dogon bayani a kan roƙonsu ga gwamnatin Kano da rundunar ƴan sandan.

Kara karanta wannan

Daga zuwa aiki a Najeriya, ɗan kasar China ya yi mutuwar da ba a saba gani ba

Yan sandan Kano sun nemi hadin kan jama'a
Jama'a sun roki ƴan sanda kan kisan Sadiq Gentle Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Al'amin El-Yakub ya ce:

"Mu na roƙon alfarma a wajen me girma gwamna AKY da ya taimaka ya ƙaddamar da dokar ta ɓaci a kan harkar daba da ƙwacen waya a jihar Kano."
"Ƴan majalisunmu su taimaka su yi dokar hukuncin kisa a kan duk wanda aka kama da ƙwacen waya ko harkar daba ko siyar da ƙwaya a jihar Kano."

Ya ƙara da roƙon wamnati da haɗin gwuiwar ƴan kasuwar waya su sa doka ta haramta siyan wayar da aka taɓa amfani da ita na wucin gadin watanni shida har sai lamari ya daidaita.

Ya ce:

"Gwamnati ta ware kuɗi na musamman don taimakawa ƙungiyoyin bijilanti na duka unguwannin jihar Kano."

Gwamnan Kano ya yi ta'aziyyar hadiminsa

A baya, kun ji cewa gwamnatin Kano ta yi jimamin rasuwar ɗaya daga cikin masu ɗaukar rahoton musamman ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sadiq Gentle.

Sadiq Gentle, wanda ya kasance matashin ɗan Kwankwasiyya, ya rasu ne a ranar Alhamis, bayan wasu ‘yan daba sun kutsa gidansa inda su ka soke shi.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce bayan an kwantar Sadiq Gentle a asibiti, ya kuma bayar da umarni ga kwamishinan lafiya da a fitar da shi ƙasar waje kafin ya rasu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng